Wani mazaunin birnin tarayya Abuja kuma mai koyar da motsa jiki da bada shawara akan cin abincin da ya kamata Olu Aijotan ya shawarci mutane musamman masu azumi da su kula da irin abincin da suke ci domin samun ingantacciyar lafiya a jikkunansu.
Ya fadi hakan ne a ranar Litini a Abuja inda ya fadakarwa masu azumi cewa ya su yawaita cin abincin da zai kara musu lafiya a jiki ba wanda zai iya illata musu jiki ba ko samar musu da rashin lafiya ba.
Ya shawarci mutane akan shan ruwa musamman a lokacin da ake bude domin shine ne jiki ke bukata kafin abinci sannan kuma idan za a sha ruwan, asha shi a natse ba cikin hanzari ba.
Ga sauran iri-irin abincin da mai azumi zai ci domin samun lafiya a jiki.
1. Cin kayan itatuwa kamar su kankana, abarba, tufa, ‘ya’yan inabi, mangwaro, da kuma makamatansu.
2. Za kuma a iya cin shinkafan da masu cutar siga ke ci wanda ake kira da ‘Brown Rice’ da ‘Basmati’ saboda yana rage kiba a jiki.
3. Za a iya cin kifi da naman kaza amma a guji naman sa.
4. Za a iya gauraya abincin da ganyayakin da ake ci kamar alaiyaho, ganyar ugu ko kuma a kwada ganye latas, lansuru,da makamantan su domin suna dauke da sinadarin dake kira ‘Vitamins’ wanda ke kara karfin garkuwan jikin mutum da kuma jini.
5. Za kuma a iya cin tuwon alkama, semo, wainan shinkafa, alale saboda suna dauke da sinadarin da ake kira ‘Protein’ wanda ke gina jikin mutum.
Ya shawarci masu azumi da su rage cin kayan zaki musamman a lokacin bude baki ko sahur domin yin hakan yakan sa mutum ya kara kiba a jiki.
Ya ce za a iya motsa jiki kadan kamar na tsawon awa daya kafin a fara cin abinci haka kuma bayan an gama cin abinci shima za a iya hakan amma a dan ba da lokaci.