A ranar Asabar sojoji su ka cafke wani babban gogarman Boko Haram, mai suna Aliyu Ahmed, da aka fi sani da “Aliko”.
Kakakin yada labaran rundunar sojojin kasar nan, Sani Usman ne ya bayyana haka, inda ya ce Bataliya ta 33 ta cafke shi a ranar Juma’a, sakamakon wani samame da ta kai a kauyen Yuga da ke cikin Karamar Hukumar Toro, a Jihar Bauchi, a wata maboya da ya lafe.
Rundunar kuma ta ce ta kama wasu masu samamen kananan yara su hudu tare da kananan yaran da suka sato har 19 a jihar Yobe.
An dai samu Aliko da zungureriyar bindiga guda daya, da kuma wata bindigar samfurin harba-ruga ita ma guda daya.
” Lokacin da ake masa tambayoyi, ya bayyana da kan sa cewa an sha kai munanan hare-hare da shi, kuma ya taba mallakar bindiga samfurin AK-47, wadda ya ce a wani hari da suka kai cikin 2016 ta salwalta.
Burgediya Janar Usman ya ci gaba da cewa su kuma masu samamen nan hudu da aka kama, Bataliya ta 120 ce kama su a lokacin da suka saci yara 19 daga Pataskuman zuwa Garin Tuwo, Bungai da kuma Buni Yadi a cikin Karamar Hukumar Gujba da ke Jihar Yobe, da kuma Galarabala a Jihar Barno.
Ya ce an damka masu samamen yaran da yaran gabadayan su a hannun hukumar hana safarar kananan yara.