Wani abin ban takaici da tashin hankali da ya auku a garin Funtua da ke jihar Katsina ya dimauta mutane da dama da suka ji labarin inda wata mata ta kama mijinta tirmi da tabarya ya na lalata da akuyar gidan.
Bata ko yi wata wata ba matar tako yanka ihu inda makwabta suka zo wurin da abin ya ke faruwa.
Bayan sallallami da koke koke da wasu suka yi magidanci mai suna Babangida ya tsaya a wurin cirko cirko kamar sabon dan Kabilar ya ce wannan shine karo na biyu da yake yin hakan da akuyar kuma idan da za a yankashi bai bai san Menene ya kai shi yin haka ba.
Babangida dai dan shekara 42 sannan yana da ‘ya’ya 6 da matarsa da a yanzu haka tana da tsohon ciki.
Rundunar ‘yan sandan Jihar Katsina ta tabbatar da aukuwan haka sannan ta ce za ta gurfanar da Babangida a Kotu.