Gamayyar Kungiyoyin matasan Arewa sun rubuta wa mukaddashin shugaban Kasa wasika domin sanar masa wasu daga cikin dalilan da ya sa suka nemi ‘yan kabilar Igbo su tattara nasu – inasu su koma yankinsu tunda sun ce su ba sa kaunar ci gaba da zama tare da musamman ‘yan Arewa.
A wasikar matasan sun zayyanu wasu hujjoji da suke bukatar Osinbajo ya duba sannan idan da hali a dauki wannan hanya domin kawo karshen wannan cece-kuce da ake ta yi tsakanin ‘yan Najeriya da ‘yan kabilar Igbo masu nemar kafa kasar Biafra.
Duk da cewa ‘yan Kabilar Igbo sun fi kowa yawa a wasu sassa na kasar nan sannan duk da irin yardar musu da akayi su zauna a yankunan sun fitini mutane da su kasar su suke so.
Sannan muna so mu tunatar da mataimakin shugaban kasa cewa zama da ake yi na awoyi da shugaban nin ‘yan kabilar Igbo din domin samarda maslaha akan wannan rikita-rikita ba zai sa ace wai an iya warware wannan matsala ba.
Sannan wani abin tashin hankali shine irin yadda shugaban kungiyar IPOB wato Nnamdi Kanu ya fito karara ya ce kungiyarsa da ‘yan kabilar Igbo din sun tanaji isassun makamai domin tunkarar duk wanda ya tsaya musu a gaba kan bin da suka sa a gaba.
Hakan yasa ba za mu ci gaba da zama kamar kurame ba sai dai ayi ta taka mu ba za muce uffan ba. Yanzu mun fito domin mu nuna cewa tunda abinda suke bukata Kenan su kama gaban su ba sai ma an zubar da jinin kowa ba.
Sannan kuma shugabannin ‘yan kabilar Igbo din sun ci gaba da mara wa shi Nnamdi Kanu baya da bashi duk irin goyon bayan da yake bukata domin samun nasara akan abinda ya sa a gaba.
ABIN DA YAFI TADA MANA DA HANKALI A AREWA
Dalilin fadi da sukayi karar cewa suna shirye da makamansu domin samun wannan kasa tasu da suke nema, muka ga ya kamata mu farga tunda wuri, kada sai abu ya lalace sannan mu sa hannu a aka. Gashi kuma sun bazu kacakaca ya yankin Arewa kamar zuma.
Ganin cewa duk da nemar kasar Biafra da suka yi a 1966 da ya jawo rasa rayukar da ba’a san iyakansu sannan kuma basu daddara da hakan ba yanzu, toh ba sai an kai ga hakan ba, muma mun hakura su tafi kawai.
A jihar Kano kawai ‘yan Kabilar Igbo na da shagunan kasuwanci sama da 100,000 inda ba wani dan Arewa ko dan kudu maso Yamma da zaka ga yana da ko da shago ne a kasuwannin su a yankin su amma duk da haka sais u fito suna ci wa mutane fuska.
Babu irin sunayen da ‘yan Kaibar Igbo basa kiran dan Arewa a arewan ma amma duk da haka an kyalesu saboda zaman tare kasa daya amma duk basu ga haka ba.
ABIN DA MUKE SO
Tunda dai akwai irin wannan doka ko kudiri da ake da ita a kundin tsari da mulkin kasashe na majalisar dinkin duniya cewa duk inda wasu suka nemi rabuwa daga wata kasa da suke zaune, akwai hanyoyi da ake bi domin warware wannan matsala ba tare da an zubda jinin kowa ba, muna Kira ga Mukaddashin shugaban kasa da ya amince da hakan a zauna domin samar da irin wannan matsaya kowa ya kama gabansa.
Kuma mu har yanzu muna kan bakar mu sannan babu abinda zai sa a zubar da jinin wani akan haka.
Suna son Biafra, mun yarda ku tafi salin alin.
Karanta a shafin mu na Turanci: Northern group, calling for exit of Igbos, writes Osinbajo; asks him to allow Biafra Republic