Wani soja ya bindige wasu mutane uku har lahira a Kaduna

0

A wani abin tashin hankali da ban mamaki da ya faru a Kaduna ranar Juma’a ya sa ana dan zaman dar-dar musamman a unguwar ‘command Junction’ dake iyaka da unguwan Sabon Tasha.

Kamar yadda wani danuwan wanda aka kashe ya sanar wa Premium Times yau ya ce sojan ya bindige dan uwansa ne mai suna Solomon a lokacin da yake dibar yashi a wata kwata dake kusa da makarantar sakandare na Command.

An ce shi dai wannan soja yana tsaye ne ya zukar tabar iblis wato ‘WeWe’ a lokacin da shi Solomon ya zo kalen yashin a wannan kwata. Bayan sojan ya umurce shi da ya bar wurin amma kafin ya tashi sojan ya fusata yako dirka masa harsashi a tumbinsa. Nan take ya ce ga duniyar ku nan.

Matasa ko da suke kusa da wurin su ka taso wa sojan daga nan ko gogan naka sai ya hau bude wata inda yayi sanadiyyar rayukan wasu matasan biyu kuma.

Da kyar dai aka samu aka tausasa matasan inda shi kuma sojan ya gudu cikin makarantar Command.

Rundunar Soji a Kaduna ta fitar da rahoton cewa lallai zata binciki al’amarin sannan ta roki matasa da mazauna unguwan da su kwantar da hankalinsu.

Share.

game da Author