“Ayye, zuwa Haji ba cin kasuwa ba ne,
*Lallai lallai dum mu na zuwa.
Alhazawan Allah na yaba maku,
*Lallai lallai sum mu na zuwa.
Dum mai sallah ya dauki aniya,
Ya tara kudin shi ya gaida Annabi,
-Marigayiya Barmani Choge
Tashin farko zan fara da sanar wa duk wanda ya karanta wannan rutubu cewa ban yi wannan rubutu don na hana wani ko ba wani shawarar daina zuwa Umra ba ne. Ba kuma na yi ne da nufin sace tayar motar wanda bai taba zuwa ba. Sannan kuma duk mai zuwa Umra a kowace shekara, shi ma ban hana shi zuwa ba. Ko ni na sake samun dama, ina son komawa.
Amma wannan duk ba zai hana ni yin tsokaci dangane da, matsaloli da bahallatsar da ake cin karo da su tattare da tafiya aikin Umra ba. Baya ga matsayi nan a mai yin sharhi, ni ganau ne, ba jiyau din halayya da dabi’un ‘yan Nijeriya a kasar Saudiyya a lokacin aikin Hajji ba. Sannan kuma yin tsokaci a kan wadannan matsaloli, ba kai na farau ba, kuma ba daga ni an daina yin tsakacin ba.
A cikin 2002, kwararren marubuci kuma mai sharhi kan al’amurran rayuwa a cikin harshen Turnci, Malam Adamu Adamu, ya yi dogon sharhi dangane da irin kwamacalar da ke tattare da tafiya aikin Umra. Da ya ke da Turanci ya yi rubutun na sa, ya sa wa maudu’in rubutun nasa suna: Memo to Umrah Returnees. Watau nasiha zuwa ga wadanda suka dawo daga Umra. Adamu Adamu shi ne Ministan Harkokin Ilmi a yanzu.
Ban san daliliba, ko Adamu gani ya yi nasihar da ya yi a 2002 ba ta kunnuwan wadanda ya yi nasihar don su ba, ko kuma gani ya yi abin da ya yi tsokaci a kai sai kara muni ya ke yi, hakan ya sa a cikin 2012 ya sake dauko waccan nasiha da ya yi, ya sake buga ta, tare da yi mata kwaskwarimar kara wasu matsaloli da badakalar da ya ke ganin ta kara muni, tun bayan wannan rubutu da ya yi.
Shekara biyar bayan Adamu Adamu ya sake maaimaita nasihar da ya yi, to ni ma na lura da cewa akwai matukar bukatar na yi nawa tsokacin, duk da dai ni ma na taba yin irin haka bayan wata dawowa aikin Hajji da nay i cikin 2009, inda na yi magana a kan bulkara da harankazamar da ‘yan Nijeriya ke yi a yayin aikin Hajji.
Idan mai karatu ya yi duba ko tsinkaye uku a lokaci guda: wato na bilyoyin dalolin da ake kashewa zuwa Umra, sannan ya dubi irin dimbin matsalolin da duniyar musulmi ke ciki, musamman irin yadda yake-yaken gaba, kiyayya, bambancin akida da kuma ta’addanci suka kassara duniyar musulmi, to ni ina ganin watakila a samu wadanda ke da ra’ayi na cewa kamata ya yi masu gasar zuwa Umra da wadanda suka maida Umra zuwa yawon bulkara a kowace shekara, kamata ya yi su hakura haka nan, su karkatar da kudaden wajen ayyukan ginawa da inganta rayuwar musulmi.
Gwargwadon karfin ka, gwargwadon gudummawar ka. Kai ka ingata rayuwar makwabcin ka. Wani ya inganta rayuwar ‘ya’ayan gajiyayyu da gajiyayyaun unguwar sa, ko garin su ko jiha baki daya.
Kiyasi ya nuna cewa cikin 2009 musulmi milyan 3.7 ne suka je Umra daga fadin duniya. A cikin 2012 kuma an ce milyan biyar da dubu dari uku, 5.3. daga cikin milyan biyar din nan, ‘yan Nijeriya dubu saba’in da biyar ne, wato 75,000, wadanda bincike ya nuna cewa wasu sun biya karamin tikitin jirgi naira dubu dari biyar, matsakaici naira milyan daya, sai kuma babban tikiti naira milyan biyu.
An yi lissafin kiyasin kudin da ‘yan Nijeriya suka kashe ya kai naira bilyan 106, 108,000,00.00 a waccan shekarar.
Wani bincike da PREMIUM TIMES HAUSA ta gudanar, ya tabbatar da cewa, wannan Umra ta 2017, mafi karancin kudi shi ne naira dubu dari bakwai. Bincike ya nuna kamfanin safarar mahajjata da Umra na AFSAN Travels and Tours sun caji naira milyan daya da dari hudu a matsayin karamin tikiti. Sannan kuma naira milyan biyu da dari daya a matsayin matsakaicin tikiti. Babban tikiti kumac shi har naira milyan biyu da rabi.
Sai dai kuma wani bincike na gane-gari da PREMIUM TIMES HAUSA ta gudanar, ya tabbatar da cewa akwai tikiti na game garin masu karamin karfi na naira 870,000,00.
A wannan shekara kuma ta 2017, an ce sama da musulmi dubu arba’in ne suka tafi Umra. Watakila ma wadanda suka je watanni biyu kafin azumi sun kusa wasu dubu arba’in din. Sannan dubu arba’in din da ke can a yanzu, a tikitin jirgi kawai banda ci da sha da tsaraba da kuma sauran bushasha, za su kashe naira bilyan 28.
Matsalolin Da Mu Ke Fama Da Su
Duk inda musulmi ya ke a fadin kasar nan, ya na bukatar agaji, musamman yadda Boko Haram ta ragargaza Arewa. A fannin tattalin arziki ma mu na a baya. A halin inganta rayuwa nan ma a baya mu ke. Masu hali kalilan ne ke bayar da dimbin dukiyar su wajen ayyukan inganta rayuwar marasa galihu. An wayi gari mu ke da matsala, amma har Turawan da ke can wata kasa sun fi mu tausayin kan mu. Kungiyoyin agajin su ne a sahun gaba wajen raba kayan agaji a kasashen musulmi da yaki ya ragargaza.
Da a ce za a rika yin wata gidauniyar inganta rayuwa, kowane mai hali a duk shekara ya zuba rabin milyan ko naira milyan daya, to cikin shekara uku sai Kano ta zama abin kwatance a duniya, Kaduna, Katsina, Bauchi da Sokoto da sauran jihohi ma haka. Za a gina masana’antu da kudaden. Matasa za su samu aikin yi, za a inganta karatu da tarbiyyar matasa, shaye-shaye za su ragu ko ma mu yi bankwana da su.
Tattalin arzikin mu zai bunkasa, harkokin noma a saukake za su inganta. Za a gina masana’antu yin takin zamani da sauran su. Za mu kuma daina wulakanta kan mu mu na zuwa har kasar Chana mu na wo odar tsinken tsire da tsinken sakace don tsananin lalacewar mu. Za mu kuma daina dogaro da hatta dan kamfai sai mu sayo daga Chana sannan talaka zai rufe al’aurar sa.
Da masu hali ko masu hannu da shuni za su yi tunanin zaman gina ingantacciyar al’umma da kudin su, ya fi alheri bisa gudummawar likafanin da suke bai wa talaka bayan ya gama cin wahalar duniya ya mutu. Ya fi ka yi ta kwasar kudi ka gasar zuwar Umra kai da abokin kasuwancin ka, ku na fariya kun a riya.
Mun kuma sha ganin yadda wasu hamshakan da su ka danne hakkin wasu, ko kuma suka cika cikin su da bashi na fitar hankali, za su dauki wasu sojojin-haya a tafi Umra a yi da du’a’i wai ana rokon Allah ya rufe bakin wanda ya bada bashin, yadda ba zai kara tambaya ba, har kasa ta nade.
Mun Ki Gudu, Mu Na Tuma Tsalle
Ganin irin yadda mu ke ka tururuwa da gasar tafiya aikin Umra a duk shekara, mutane da daman a korafin irin dabi’u da halayyar mu idan mun ji aikin Hajjin shi kan sa ko kuma Umra. Idan ka tsaya ka yi duba, maimakon idan mutum ya dawo ya natsu ya nisanta daga wasu munanan halaye, sai ma ya sake tsunduma a cikin wasu manyan munanan, sama da na baya.
Abin haushi kuma shi ne yadda manyan ‘yan siyasa da manyan ma’aikatan gwamnati da masu mulki suka maida Umra wata mahadar zaunawa a yi taruka na sirrin kisisina da sauran tuggun siyasa.
A duk shekara, yawancin gwamnoni musalmi duk su na Umra, ministoci, haka sanatoci da ‘yan majalisar tarayya da na jihohi da sauran manyan kusoshin gwamnati. A yi sati biyu ana addu’o’i, amma da an dawo a ci gaba da harkalla da kashe-mu-raba da dukiyoyin al’umma.
Yawanci a dandalin zama, rukuni ko gidajen kwana da otal otal din da ‘yan Najeriya ke zaune ne za ka ji ana zurfa ashariya da sauran zancen batsa kala-kala, irin wanda sai a Gidan Magajiya za ka ji irin su.
Inda ake yaudadrar kai s i ne yadda barayin gwamnati ke zuwa a duk shekara su na yin tubar-muzuru. Ka saci kudi ka kimshe, duk shekara ka na zuwa ka na sallah da dawafin neman gafara. Maimakon idan ka dawo ka sauya halayen ka daga mummuna zuwa kyakkyawa, sai ma ka sake dulmiya a cikin wata sabuwar harkallar. Wata harkallar ma tun a can Saudiyya za a kullo ta, a dawo gida Nijeriya a warware ta.
‘Yan Bulaye, ‘Yan mata Da ‘Yan Raraka
Wato su kuma wadannan matafiya Umra din, akasari wasu su ka matsa wa lamba su biya musu. Babban muradin su kawai shi ne su je Umra su hadu da manyan mutane, wadanda ganin su a nan Najeriya ya nay i musu wuya, amma sun san juna kafin wannan ministan ko gwamnan ya samu mukami, ko kuma ko da bayan ya samun ne.
Su na yi iyakar kokarin su su gano otal otal din da manyan masu rike da mukaman siyasa su ke zaune, domin su je su gaida su, daga can a ba su daloli ko kuma Riyal. Idan mai karatu wanda ya taba zuwa aikinn Hajji zai yi tsinkaye, zai fahimci cewa ko a lokacin aikin Makka, yawanci manyan kusoshin gwamnati da ba su fashin zuwa Hajji, ba su zama cikin Makka, sai dai su yi kwanciyar su a Jedda, su lamfale, sai ranar fita daga Makka zuwa Minna, sannan z aka rika ganin su na ta antayowa tururuwa guda su na shiga cikin Minna.
A lokacin Hajji ma haka ‘yan raraka ke hawa motoci su tafi Jidda, su yini sun a bulayen neman gwamnonin su da wasu manyan ‘yan siyasa domin su yi raraka.
Mu je Haji dakin Nana Fatsima,
*Lallai lallai dum mu na zuwa.
Ta-Audu na yi hura, na cura nakiya,
*Lallai lallai dum mu na zuwa.
Wa ma adareka wa aali rabbuka,
*Lallai lallai dum mu na zuwa.
Ta-Audu kin ji karatun saida nakiya,
*Lallai lallai dum mu na zuwa.
Amma wani na nan yai shirin Haji,
Ba kayan ka ba na rataya,
-Marigayiya Barmani Choge
Su ma ‘yan mata akasari wadanda sun fi karfin kwana a gidan iyayen su da ke zaman ciyar da kan su, sun maida Umra wata mahadar haduwa da manyan samarin su. Wasun su dama a ladan-gabe suka samu kudin tikitin jirgin zuwa Umra, ba da gumin goshin su ba. Don haka sun maida Umra wurin haduwa da wane da wane, wadanda ganin su a can kan sa ki samu babbar kyauta wadda idan kin hada da kyautar dalolin Alhaji wane da na Oga wane ko Riyal din gwamna wane, zaki ma iya ciko dankareren buhu da gumama, ki dawo Nijeriya kin a ‘biznez.’
Tabbas akwai masu zuwa aikin ibada. Amma fa daya akwai masu zuwa Umra da Haji, wadanda mutum ko ba alkali ba ne, idan ya gani ko ya ji abin da su ke aikatawa, lallai zai ce kawai dai Hajijiya wasu ke zuwa.
Idan mun koma kan Saudiyya, abin takaici ne yadda a duk shekara milyoyin musulmin duniya ke samar mata kudin shiga ta hanyar zuwa ayyukan Hajji da Umra, amma ita kuma sai ta rika karkatar da dukiyar kasar wajen sayen muggan makamai na bilyoyin daloli a duk shekara ana ta kashe-kashe a cikin kasashen musulmi.
Su kuma manayan malaman mu, a duk shekara su ma sun a Umra ko aikin Hajji. Idan an hadu a can kowa musulmi ne, kowace akida ya ke yi. Amma da an dawo nan Nijeriya kowa sai ya shata kan iyakar kafirta juna. Sai ka ce ba su ne suka rika cewa juna ‘Salam alaikum’ a Saudiyya ba.
Abin lura shi ne ba jiya ko yau aka fara fama da irin wadannan matsalolin ba. Kusan shekaru talatin baya, Barmani Choge ta yi wannan tsokacin a cikin wakar ta “Lallai lallai dum mu na zuwa,” wadda na kawo can a sama.
Gambu mai wakar barayi ma da wani barawo ya biya masa aikin Hajji, har ya ce ba zai karba ba, sai matar sa ta zuga shi ya karba ya hau jirgi ya tafi.
‘’Ka na bisa, iska na bugun ka,
Ko ba da lada babu laihi,
Ba ka dai kashe ko sisin kwabo ba.”
-Inji Gambu.