Tsakanin Soba da Tahir: Kotu tayi watsi da bukatar Hon. Musa Soba, ta daga zama zuwa 4 ga watan Yuli

0

Babban kotun tarayya da take zamanta a Kaduna tayi watsi da bukatar da Hon. Barrister Musa Soba ya shigar ya na neman kotun ta kada ta amince da shaidun da Dr. Tahir ya shigar yana kalubalantar cancantar tsayawa takaran da Barr. Soba yayi a shekara 2014.

Barrister Soba na wakiltan yankin Soba, jihar Kaduna a majalisar wakilai.

Kotun ta ce Dr. Tahir ya na da hakki bisa shari’a da ya nemi yin kara ga takardunsa da ya shigar a gaban kotun duk da yayi jinkirin hakan da kwana daya.

Bayan haka Barister Soba ya roki kotin da ta daga sauraren shari’ar domin ya kammala nazari akan nashi hujjojin da bayyana su a gaban kotun.

Alkalin Kotun ya daga ci gaba da shariar zuwa 4 ga watan gobe.

Share.

game da Author