A wani nazarin gani da ido da wakilin PREMIUM TIMES HAUSA ya yi, ya bi titin Kaduna zuwa Kano, inda ya fara kididdigar manyan ramukan kan titi masu zurfi wadanda ke haddasa munanan hadurra a kan titi.
Daidai lokacin da ya isa dab da shiga garin Kwanar Dangora bayan ya wuce Zaria, ya samu wata motar kamfanin Coca Cola ta yi hadari, kuma ana ta faman tattara kwalaben Coca Cola na roba.
Bayan ya gama ba idon sa abinci daga nan sai ya ci gaba da lissafa manyan ramukan da ke kan titi, tare da kidaya motocin da suka yi hadari da ke can gefen titi a kwarangwatse.
Daga Kwanar Dangora zuwa Ciromawa, tafiyar ba ta wuce kilomita saba’in ba, amma an lissafa manyan ramuka masu kayar da mota komin girman ta, har guda 170. Ba su kenan ba, ya daina lissafawa ne soboda Magriba ta dan shuda, duhu ya fara.
Wannan kididdigar dai ta hannu daya ce, daga Kano zuwa Zaria.
Shin sai yaushe za a kawo karshen asarar rayuka da dukiyoyin da ake yi tsakanin Kano da Zaria?