Titin Abuja zuwa Kaduna: Lahirar Matafiya

1

A yanzu dai babu sauran wani boye-boye ko wata kwana-kwana. Duk mai hankali, ko ma wace jam’iyya ka ke goyon baya, tilas ka fito ka yarda da cewa a nan yankin Arewa-maso-Yamma, matsalar tsaro dai kusan ba a rabu da Bukar kenan za a ce.

Domin yayin da muke ta murnar an kakkabe Boko Haram a wannan yanki kama daga Jigawa, Katsina, Kano, Kaduna har Zamfara da Sokoto, to yanzu kuma ga wata sabuwar matsala nan, ta kunno kai, ta na nema ta gagari hukuma, ko kuma kawai a ce hukuma na gani, amma an ki tunkarar matsalar gadan-gadan a yi mata kwaf-daya kowa ya huta.

Masu garkuwa da mutane na neman hana zirga-zirga tsakanin Kaduna da Abuja. Wannan ba karamin bala’i ba ne, amma an sa ido abin na kokarin ya gagari hukuma. An kau-da-kai, ba a tunanin kada matsalar ta zama game-gari a Arewacin kasar nan, har ta kai cikin kowane lunguna ka kauyuka. Duk abin nan, gwamnati fa ta sani.

A kowace rana ana samun rahoton an tare matafiya a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna, ko Kaduna zuwa Abuja, an sace su, an shiga daji, an yi garkuwa da su ana neman a biya fansar ran su da milyoyin nairori. Duk abin nan gwamnati ta sani.

Kafin abin ya yi muni sosai, masu garkuwar kan tsaya su darje, sai sun zabi mota mai kyau, mai tsada, wadda suke yi wa kallo da tunanin mai motar ko dai attajiri ne, ko ma’aikacin gwamnatin da ya tara, ya kimshe dukiya ko kuma ma ko da dan uwa ne ga wani ko wasu masu hali. Duk abin nan, gwamnati ta sani.

Amma abin takaici, yanzu masu satar mutane a kan titin Kaduna zuwa Abuja, sun daina tsayawa bata lokacin zabe, hatta manya da kananan motocin haya duk tarewa ake yi, sai su zabi wani ko wata mai alamar kitse-ga-rogo, su damke su darkaka cikin daji da su. An yi garkuwa da su kenan. Duk abin nan, gwamnati fa ta sani.

A baya sai cikin dare daga magariba su ke fara tare motoci. Amma yanzu sun kamo hanyar gagarar hukuma. Su na tare hanya da safe, da rana kata ko da yammaci. Kuma abin mamaki, su na tsayawa kan titi ne, kamar yadda ‘yan fashi da makami ko VIO ko ‘yan sanda kan tsaya su na binciken motoci. Kuma gwamnati ta san da haka. Jami’an tsaro ma sun san da haka. Duk abin nan, gwamnati fa ta sani.

Inda abin ya ke ban-haushi, shi ne yadda kiri-kiri ake neman a bar talaka ya kwan-ciki, domin yanzu manyan masu fada-a-ji a gwamanati sun fara kaurace wa titin. Su da iyalan su dai dai su hau jirgi daga Sokoto ko daga Kano ko daga Kaduna. Idan ma ba a yi maganin abin ba, to an kyale bala’in a kan talakan da ya sadaukar da ransa da lafiyar sa, har ma da dukiyar sa wajen zaben shugabanni ‘yan-gangan kenan.

Babban rashin kyautawar gwamnati a nan shi ne, da ya ke ta san halin da hanyar ke ciki, lokacin da ake gyaran filin jirgin Abuja, aka maida jirage su na tashi da sauka a filin jirgin Kaduna, sai aka zuba jami’an tsaro birjik dauke da manyan makamai a kan titin, tamkar dai yadda Isra’ila ke zuba sojoji a kan iyakar ta da Falasdinu. Ba don komai ba saboda komai girman ka duk mukamin ka, idan aka sauke ka a Kaduna, to mota za ka hau ka karasa Abuja. Haka daga Abuja ma mota za ka hau zuwa Kaduna.

Kafin nan, a baya titin Kaduna zuwa Abuja a lalace yak e, kullum sai ya ci rayukan matafiya, saboda yawan ramuka. Ba a tashi cike ramukan ba, sai da aka ga manyan masu-fada-aji za su rika zirga-zirga a kan titin daga filin jirgin saman Kaduna zuwa cikin Abuja, ko kuma daga cikin Abuja zuwa filin jirgin sama nass Kaduna.

Sai dai kash! Ana kammala gyara filin jirgin Abuja, sai aka janye mafi yawan jami’an tsaron da aka zuba. A da fa lokacin da manyan masu mulki ke bi hanyar, kafin a kammala gyaran filin jirgin Abuja, har jirgin sama samfurin helikwafta ke shawagi a kan titin, dauke da jami’an tsaro a ciki, don dai kada masu garkuwa da mutane su sace wani dakaren gwamnati.

‘Yan kalilan din ‘yan sandan da ke sintiri a kan titin Kaduna zuwa Abuja yanzu, duk burga ce kawai, hakorin zomaye ne, ba su iya cizon kowa. Ko kuma ma a ce duk magen-Lami ne, ba cizo ba yakushi. Dalili, a kullum ana tare matafiya a na yin garkuwa da su, ba za ka taba jin cewa ‘yan sandan nan sun fasa garken masu garkuwa da mutane, ko sun damke su ba. Kuma duk gwamnati ta sani.

Kullum dai labarin biyu ne, ko dai an sace matafiya ko kuma an sako wanda aka sace, amma ba za ka ji labarin an kamo masu garkuwa da matafiya a kan titin Kaduna zuwa Abuja ba. Duk abin nan gwamnati ta sani.

Kai sai ka rasa yadda ake masu garkuwa din nan ke cin karen su babu babbaka a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja, tafiyar kilomita 166 kacal daga Kaduna zuwa Zuba. Sannan kuma akwai kyauyuka a kan titin sun kai arba’in. Sannan abin takaici, duk wanda za a yi garkuwa da shi ko a can kusa da Kaduna ko a cikin dajin Jere zuwa Bwari, to a cikin Jihar Kaduna ake yin garkuwar. Kuma duk gwamnati ta sani.

Da za a tara sunayen mutanen da aka yi garkuwa da su a cikin shekara biyu din nan, a hada su da sunayen wadanda suka yi gudun-famfalaki a tsakar dare suka tsira, da kuma yawan matafiyan da suka kwana a kan bishiyoyi bayan sun gama gudun tsira daga mahara, to sunayen da za a tara sun sun firgita mai karatu.

Kaico! Da ya ke yanzu akwai jirgin kasa na zamani, daga Abuja zuwa Kaduna, ko daga Kaduna zuwa Abuja, sai mu ka wayi gari manyan ma’aikatan gwamnati da shugabannin da muka sha rana muka yi wa kamfen muka zabe su, yanzu sun fara murje idon rashin kunya da rashin tausayi, sun koma su na hawan jirgin kasa zuwa Kaduna daga Abuja, ko kuma zuwa Abuja daga Kaduna. Saboda rashin kunya ma har da jiniya za ka ga an rako iyalin wani dakaren Abuja ko shi kan sa zuwa filin jirgin kasa.

Shi kan sa wannan jirgin kasa da aka ce an yi shi domin a saukake wa talaka zirga-zirga, abin ba haka ba ne, kuma ba gaskiya ba ne. Na farko dai idan talaka ya hau mota daga Abuja a tashar Jabi ko Mabushi zuwa Kaduna, to naira 1500 zai biya. Idan kuwa ba sauri ya ke yi ba, ko kuma aljihun sa babu nauyi, zai hau motar naira 200 zuwa Zuba. Daga can sai ya samu mai sauki ta naira 800 ko 700 zuwa Kaduna.

Amma idan mutum ya tashi daga Abuja zai je tashar jirgin kasa, to sai dai ka dauki shatar taksi, kuma ba wanda zai kai ka a naira 1000, sai dai dubu 2000. Ko kuma idan ka na da mota wani ya tuka ka ya kai ka. Kuma sai ka yi asubanci tamkar ladani sannan za ka samu jirgin, saboda a nesa da gari aka yi tashar.

A cikin jirgin kasa gwamna ne kadai ba za ka ci karo da shi ba, amma har tsoffin ministoci da tsoffin su wane da wane da kuma manyan masu masu mulki a yanzu, kai har tsohon ministan tsaro duk za ka gani, ko su ko iyalan su. Kowa ya yi mursisi, an bar titin Kaduna zuwa Abuja a hannun masu garkuwa da jama’a. Kun gani ko? Ashe dai tabbas gwamnati ta sani.

Hausawa na cewa gaba damisa baya siyaki. Sai ka na murna ka hau jirgin kasa daga Abuja ka sauka Kaduna, idan za ka karaso Kano kuma nan ma wata sabuwar wahala ce. Kiri-kiri ana gani an bar titin Zaria kuwa Kano ya lalace. Idan za ka Kano daga Zaria sai ka lissafa manyan ramun da ke kayar da manya da kananan motoci sun fi 300. Haka ma idan ka taso daga Kano zuwa Zaria, manyan ramuka sun fi 300. Da ka yi tafiya kadan kuma za ka samu mota ta fadi, wata ta kife, wata ta hantsila daya tsallaken, wata ta bintsire, wata kuma ta yi kaca-kaca.

Ga shi dama Bahaushe ya ce ba a bari a kwashe daidai – ko dai ka iske fasinjoji sun tsira amma mota ta lalace, ko kuma ka iske mota ta lalace amma an yi asarar dimbin dukiyar da ke ci, ko kuma ka iske an yi asarar rayuka, dukiyoyi da kuma motar. Kuma duk gwamnati ta fa sani!

Tabarbarewar tsaro a kan titin Kaduna zuwa Abuja fa ta yi munin da an wayi gani matafiya sun fara daina jin tsoron gamuwa da ‘yan fashi. Kowa ya fi jin tsoron yin arba da masu garkuwa da mutane. Kaico! An fatattaki ‘Bukar’ amma ga ‘Habu’ ya zama dan sababi a tsakanin Kaduna zuwa Abuja. Kuma duk gwamanti ta san da shi fa!

A daidai lokacin da na ke wannan rubutu, da ya ke gwamnati na sane da irin Barnar da masu garkuwa da matafiya ke yi a tsakanin titin Abuja zuwa Kaduna, ta yunkuro ta kafa ‘yan sandan suntiri a kan titin, har su 600. Ashe dai gwamnatin ta na sane kenan.

Wannan kuwa matukar za a bai wa abin muhimmanci, to za a samu nasara, musammam idan mu ka yi la’akari da cewa kwanaki uku bayan kafa rundunar ‘yan sandan, an bada rahoton yadda sojoji suka samu galabar damke wani babban dan fashin da ya addabi matafiya wajen yin garkuwa da su a kan titin.

Sai dai kamar yadda Hausawa ke cewa ba girin-girin ba, wai ta yi mai. Idan ba a manta ba, cikin 2016 wannan gwamnatin ta taba kafa irin wannan rundunar ‘yan sandan sintiri a garin Jere, it ma har su 600. Amma abin mamaki sai tasirin rundunar ya yi tashin kumfar gishirin Andurus, tun ba a je ko’ina ba. Haka masu garkuwa da jama’a suka rika sagarabtu a kan titin su na satar matafiya. Kun ga ashe dai gwamnati ta sani kenan.

A yanzu dai babu wani dalilin da zai sa a ce wadannan zaratan ‘yan sanda da aka yi bikin kaddamarwa a garin Rijana, a ce kuma sun kasa magance wannan matsala ta satar matafiya a na garkuwa da su. Dalili, a ranar kaddamarwar sai da Mataimakin Sufeto Janar na ‘yan sanda ya koda su sosai cewa sun samu horo a kan irin wannan aiki.

Share.

game da Author