Yau Laraba ne Kungiyar Hausawan Afrika ta gudanar da taron bajekolin abincin Hausawa tantagarya a Kano. Taron wanda aka gudanar da harabar Gidan Tarihi, wato History and Culture Bureau, wanda aka fi sani da Gidan Dan-Hausa, ya samu halartar jama’a daban-daban ciki har daga Katsina, Sokoto da wasu jihohin kasarnan.
Shugaban taro Dakta Koguna, ya bayyana cewa sun kafa wannan kungiya ne ganin cewa duk sauran kabilu su na da kungiyoyin kare muradun su, shi ya Sa suka yanke shawarar kafa wannan kungiya.
Ya ce Hausawa kabilu ne masu tasiri a Afrika, shi ya sa za a hadu a tattauna tasiri da matsalolin al’adun su, sanin abincin su na aihini da kuma sanin tushen su.
Babban bako mai jawabi, Dakta Aliyu Isma’la Disu, ya gabatar da dogon jawabi inda ya fede yanayi da matsalolin auratayyar Bahaushe, bayan ya fara fayyace asalin Hausawa da kuma al’adun su da sana’o’in su na farko.
Da ya ke magana kan yadda ake gane saurayi ko budurwa sun isa aure a rayuwar Bahaushe can asali, Disu ya ce iyaye na dauka cewa idan yarinya ta fara yin fitsari mai karfi har ya na huda kasa, sai Bahaushe ya ce “ta isa aure.”
Namiji kuwa a ta bakin Disu, ya ce idan an fahimci saurayi na iya yin noma tare da yayyen sa, ko kuma ya na da jimirin zuwa kiwo ko farauta, sai a ce “yaro ya isa aure.
Daktan wanda hazikin manazarcin Hausa da Hasawa ne sosai, ya kuma bayyana irin yadda neman auren Hausawa ya canja yanzu, sabanin Hausawan can baya.
Daga nan sai ya fara ragargazar yadda Bahaushe bai dauki aure da muhimmanci ba, inda ya rika bayar da bayanan yadda Bahaushe ke yawan sakin aure.
Disu ya rika dauko yanayin zaman auratayyar Hausawan garuruwa daban daban ya na fayyace irin yadda su ke rike matan su, inda kuma ya bada misalin yadda auren Babarbariya ya ke da wahala ga Bahaushe.
Diso ya nuna matar Bazazzagi a matsayin mace mai biyayya saboda ta na tausayin irin wahalar da mijin ta ke yi a gona da sauran mu’amaloli. Dalili kenan ta ke tausaya masa.
It’s kuwa matar Bakatsine, akwai ta da fitowa gaba-gadi ta tunkari mijin ta idan ya saba mata. Ba ta da kawaici, saboda dama yawanci aure ne wanda aka a idan aka big salsala, za iske cewa tushen su daya.
Matar Basakkwace kuma zai rika ciyar da ita bakin karfin sa. Za ka ga Bahaushen Basakkwace afujajan, amma matar sa garsakekiya, mai jin dad I, amma kuma maras godiya ga miji.
Bahaushen Bauchi a ta bakin Daktan ya ce ya cika auren kabilun da ke kewaye da shi, shi ya sa ya ke tamkar mai fuskokin al’adu da dama, babu daya kwakkwara.
Diso ya karkare da bayar da dabi’ar Bakano, wanda Barebari ba su dauke shi mijin kwarai ba. A nan had ya buga misali da labarin wata Babarbariya da ta auri Bakane, aka sayo mata naman miya. A tunanin ta mage za a ba daman, domin su a Barno sun saba ana yanka rago kowa ya ya koshi.
A taikaice dai ya nuna Bahaushen Kano, mutum ne mai kwangen kudin cefane, amma kuma mai ha’intar matar sa ya na fita ya na cin abinci mai dadi.
Premium Times Hausa ta zanta da wani matashi a wurin taron mai suna Usman, wanda ya ce, ya san Hausawa na da matsalar aure, amma ya tabbata rayuwar auren wasu kabilu da dama ta fi ta Hausawa muni.
Yawancin mahalarta taron sun he da abinci dafaffe iri daban-daban, wadanda aka kai wurin taron daga garuruwa da dama. Daga cikin abincin akwai tuwo, fura, zogale da dafaffe da kuma kwadadde da sauran nau’ukan abinci kala-kala.
Takaitaccen tarihin Gidan Dan-Hausa
Gidan Dan-Hausa ya samo asali ne daga sunan wani Bature wanda ya fara kafa karatun boko a Kano, cikin 1909. Baturen mai suna Hanns Vischer, shi ne ake kira Dan-Hausa, kuma shi ne ya kafa makarantar, inda ya fara da dalibai 209 kamar haka:
1. Kano dalibai 59.
2. Neja daliabai 40.
3. Muri dalibai 25.
4. Barno dalibai 17.
5. Benuwai/Filato 13.
6. Nassarawa 13.
7. Zazzau 12.
8. Adamawa 11.
9. Ilorin 6.
10. Sakkwato 6.
Asalin Dan-Hausa Baturen Holland ne, sai zama ya kai shi Ingila, ya dade har ya zama dan kasar Ingila. An haife shi a 1846, ya yi zama a Tripoli ta kasar Libiya kafin zuwan sa Kano.
A Dakin Tarihin da ke cikin gidan, Premium Times Hausa ta ga wasu kayyayyakin tarihi da suka hada har da wasu manyan tukane da aka ce an hakkake an gina tukanen fun kafin zamanin haihuwar Annabi Isa (A.S).