Matsayin wanda yayi zina a watan Ramadan bayan an sha ruwa – Imam Bello Mai-Iyali

0

TAMBAYA: Menene matsayin mutumin da yayi zina a watan ramadan bayan an sha ruwa?

AMSA: Alhamdu lillah, Tsira da Amincin Allah su tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammad SAW.

Zina dai haramun ne, kuma zunubi da ga cikin manyan zunubbai, mazinaci dan wuta ne, hukuncinsa ya bar zina kuma ya tuba zuwa ga Allah. Kar ya kuskura ya mutu a matsayin mazinace.

Zina Lafi ne mai girma, Allah Ya ce “ Kar ku kusanci Zina, domin ita Alfasha ne kuma mummunar tafarki ne” (Suratul Isra’i Aya ta 32).

Bukhari da Muslim sun ruwato ce annabin tsira (SAW) ya ce : Mazinace bai da imani a lokacin da yake zina. Idan shari’a ta kamashi da laifin zina, to, hukuncin sa she ne ayi masa BULALA DARI, IN BAI DABA AURE BA KO A JEFE SA IN YA DABA AURE (suratun- Nur aya ta 2). Amma in Allah ya rufama sa asiri, to, ya yi saurin tuba ga Allah.

Babu shakka a cikin girma da Alfarman watan Ramadan, watane da ake nisantan muyagun laifuka manya da kanana, kuma ake rige-rige cikin ayyukan kwarai, irin tsayuwar dare, sadaka, ciyarwa.

Amma ka ga zina a cikin Ramadana tafi tsananin zunubi da girman ukuba fiye da zina a cikin watan da ba shi ba, don zunubin sabo yana kara girma da muni idan aka aikata shi a wani wuri ko lokaci na musamman.

Kamar yadda aikin kwarai yake kara lada da daraja a lokuta da gurare na musamman.

Wajibi ne ga wanda ya fada cikin wannan hadari ya yi gaggawan tuba, ya yawaita Istigifari, ya yawaita aiyukan alhairi, domin kyawawan aiyuka suna kankari muna na, kuma mai yawan tuba kamar mara zunubi ne. Allah mai yawan gafara ne kuma mai karban tuba.

Share.

game da Author