Sojojin kasar nan sun tarwatsa wani kwanton-bauna da Boko Haram su ka yi, inda har suka samu nasarar kashe wani jagoran su mai suna Abu Nazir, da kuma mabiyan kungiyar da dama. Wannan nasara dai ta samu ne ta hanyar hada karfi da sojojin suka yi tare da wasu zaratan ‘yan sa-kai, wato ‘yan vigilante ko Civilian JTF.
Kakakin yada labaran askarawan Nijeriya, Sani Usman ne ya bayyana cewa sai da aka yi ba-ta-kashi na wasu ‘yan mintina a kusa da kauyen Jarawa da ke cikin karamar hukumar Kala Balge ta Jihar Barno, kafin daga bisani ‘yan Boko Haram din da suka rage din suka arce.
Wannan artabu dai sojojin Bataliya ta 22 ce da ke karkashin shirin Operation Lafiya Dole, suka yi nasarar kashe Boko Haram din, tare da matasa farar hula na JTF, a ranar Lahadi da ta gabata, 11 Ga Yuni, 2017.
Bayan nasarar kashe Abu Nazir da rundunar sa, sojojin Nijeriya sun kuma bayyana cewa sun kama bindiga samfurin AK-47, bindiga samfurin mai baki biyu, wani bam da kuma baburan hawa uku. Sun kuma ceto wasu kananan yara 9 da Boko Haram suka sace, kuma suke ba su horo a sansanin atisayen su da ke kilomita daya kafin kauyen Jarawa.
Tuni dai wadanda aka ceto din sun a nan sojoji nay i musu agajin gaggawa, kafin a kai ga damka su a sansanin ‘yan gudun hijira da ke Kala Balge.