Ministan Makamashi, Ayyuka da Gidaje, Babatunde Fashola, ya yi wa shugabannin yada labarai na Sanatoci da na mambobin majalisar tarayya kudin goro, inda ya ce suna da Karancin sani.
Hakan ya biyo bayan cece-ku-cen da suka yi masa inda suka zarge shi da yin asarkalar kudaden ayyuka a cikin kasafin 2017.
A wata sanarwa da mai ba shi shawara a kan Harkokin Yadda Labarai, Hakeem Bello ya fitar, ministan ya ce ya nuna damuwar sa a kan yadda kakakin yadda labaran biyu suka kasa yi wa jama’a cikakken bayanin yadda majalisa ta guntule ko ta rage adadin kudin kasafin Ma’aikatar makamashi, ayyuka da gidaje da ma sauran ma’aikatu.
Idan ba a manta ba, a wani taron manema labarai, ministan ya nuna damuwar sa dangane da yadda majalisa ke rage wasu ayyuka, bayan sun sha kiran ministoci su bayyana a gabansu domin basu bayanai kan yadda kasafin kowane aiki yake dalla-dalla.
Fashola ya nuna damuwa akan yadda aka dagula kasafin ma’aikatun sa, wadanda suka shafi babban titin Ibadan zuwa Legas, titin Bodo zuwa Bonny, Kano-Maiduguri, babbar gadar Kogin Neja da kuma aikin hasken lantarki na Mambilla.
Dukkan kakakin yada labarai na Majalisar Dattawa da ta Wakilai, sun maida masa kakkausan martani inda su ka zarge shi da boye bayanan wasu kwangiloli da ba a yi a baya ba, na 2016, wadanda ya sake cusa su a kasafin 2017, ba tare da yin bayani a cikin kasafin kudi ba. Da ya ke bayani dalla-dalla, ya ce zargin titin Ibadan zuwa Lagos da suka ce aikin hadin gwiwa ne da ba haka ba ne, ya ce yarjejeniyar ce kawai da aka yi cewa lamuni ne daga banki kuma a cikin kasafin kudi za a biya su, ba wai kamfanoni ko bankuna ne za su gina titin ba.
Ya ce batun kasafin 2016 da suka ce ya na dauke da aikin gadar Kogin Neja, ya ce sun jahilci abin, domin a wancan lokaci kiyasi ne kawai aka yi, ba zunzurutun kudin ba ne aka bayar ko aka fitar da sunan aiki. Don haka a cewar Fashola, batun an ware kudin aikin tun a kasafin 2016, amma ba a yi ba, sai kuma aka sake dawo da aikin cikin kasafin 2017 bai ma taso ba.
Ya ce ai sun fi kowa sanin cewa kasafin kudi fa ba tsabar kudin ba ne a kasa zube. Kawai kiyasi ne da kirdado na abin da ake so a kashe a wani fanni ko fannoni.
“Don haka Ma’aikatar Kudi ba ta ba mu ko sisi don yin aikin gadar Kogin Neja ta biyu ba, ballantana a ce na karba na kashe ko na boye.” Inji Fashola.
Dangane da aikin lantarki na Mambilla kuwa, Fashola zargin da suka yi na cewa sun rage kudin ne saboda wai shi Fashola ya “dankara naira bilyan 17 a wajen gwaji da bincikin yanayin kasar Mambilla, ya ce an yi kwakyariya, domin akwai yarjejeniyar da aka k’ulla da China-EXIM wanda shi ne zai zai bada lamunin yin ganin wurin samar da lantarkin.
Ya ce kamata ya yi kafin su zabtare kudin su sanar da shi, ba sai bayan sun zabtare ba su koma bayan idon sa su na kutunguiwa da annamimanci a kan sa ba.
A haka dai ministan ya bi sauran zarge-zargen da suka yi masa dalla-dalla ya na maida martani.