Shugaban kungiyar fafutukar neman kafa kasar Biafra MASSOB Ralph Uwazurike ya roki matasan Arewa da su suyi hakuri a zauna lafiya tare a Najeriya.
Ralph Uwazurike ya jagoranci shugabannin ‘yan Kabilar Igbo ne zuwa garin Kaduna in da ya ce ya zo ne domin ganawa da kungiyoyin matasan Arewa domin ayi sulhu.
Ya ce kungiyarsu na MASSOB babu ruwanta da Nnamdi Kanu mai fafutukar kafa kasar Biafra domin shine ya kafa gidan Rdiyon Biafra sannan ya mika masa jagorancinta amma kafin ya ankara ‘yan siyasan yankin sun mai da ita wata kafa domin tada hankalin Mutane.
Nwazurike ya yi alkawarin za su kare mutuncin duk wani dan Arewa da yake yankin Kudu Maso Gabas.
Tsohon Shugaban mai ba tsohon shugaban kasa Janar Sani Abacha tsaro Manjo Al-Mustapha ya yi kira ga gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai da ya mai da takobin ya janye kira da yayi a kama shugabannin kungiyoyin Matasan Arewa da suka ba ‘yan kabilar Igbo wa’adin watanni uku su tattara inasu-inasu su koma yan kinsu.
Al-Mustapha ya yi kira ga matasan da su dinga tauna duk abin da zasu fadi kafin su furta saboda kada ya jawo irin wannan cece kuce ko kuma tada hankalin ‘yan Najeriya.
Manjo Almustapha ne ya jagoranci ganawan da matasan Arewa.