Sanata mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya, sanata Shehu Sani ya kaddamar da ciyar da masu Azumi abincin buda baki a fadin jihar.
A makon da ya gabata ne wasu daga cikin mazauna garin Kaduna su kayi kira ga gwamnatin jihar da ta agazawa masu Azumi ganin yadda mutane ke fama da wuyar rayuwa.
Wani mazaunin garin Kaduna, Garba Ali ya sanar wa Premium Times Hausa cewa sanata Shehu Sani ya fara ciyarwar ne tun farkon Azumi.
” Ai mu kakarmu ta yanke saka saboda tun da aka fara Azumi muke cin lagwada kyauta daga sanatan dake wakiltar mu, wato Sanata Shehu Sani. A gaskiya ya kyauta sosai.”
Ya kara da cewa yanzu hakan ana kaiwa unguwa unguwa ne domin ba masu Azumi suyi buda baki kwanukar roba.
Shima dan majalisa mai wakiltar Kaduna ta Kudu a majalisar Wakilai Rufai Chanchangi ya yi irin wannan rabo ga mutanen mazabarsa.
Rufai ya rabo buhuhunan Shinkafa, Gero, Siga da dai sauransu.