Sanata Dino bai samu tarbiyya na kwarai daga gida ba – Gwamna Yahaya Bello

0

Kiyayyan da ke tsakanin Sanata mai wakiltan Kogi ta Yamma Sanata Dino Melaye da Gwamnan jihar Yahaya Bello sai kara gaba yake yi ba yaba.

Bayan zargin gwamna Yahaya Bello da sanata Dino ya yi cewa shine ya aiko wasu ‘yan bindiga su kashe shi a wata hari da suka kai masa lokacin da yake gudanar da wata zanga-zanga a jihar, ya kuma kalubalanci gwamnan da ya fito ya bada bayanai akan yadda yake kashe kudaden jihar.

Da yake zantawa da manema labarai a Abuja, gwamnan Yahaya Bello ya ce rashin samun tarbiyya na kwarai ne ya sa sanatan ke yin abin da ya ga dama.

“ Idan mutum bai sami tarbiyya na kwarai ba zaka ga ya zama fitina ga al’umma. Idan kuma al’umma suka kasa canza shi sai kaga ya gagare su. Daga nan ne fa dole sai gwamnati ta sa hannu wajen seta shi.

Ko da yake shima Sanata Dino ba kanwan lasa bane domin yayi wa Yayaha Bello tatas a majalisa ranar Laraba inda yace gwamnan bai san abinda ya keyi ba kuma ya roki majalisar da ta kafa dokar ta baci a jihar.

Share.

game da Author