SALLAH: Gwamnatin Kaduna ta rufe Kofar Gamji, filin Murtala Square da duk wani wajen shakatawa

0

Gwamnatin Jihar Kaduna ta ce ba za a bude duk wani wajen shakatawa da ke jihar ba a lokacin bukukuwar Sallah.

Za a rufe wurare kamar su kofar Gamji, filin Murtala Square da sauransu daga karfe 6 na safen Sallah zuwa tsawon kwanakin da za a yi ana shagulgular Sallah.

Shugaban rundunar ‘Operation Yaki’ kuma mai ba gwamnan jihar Kaduna Shawara akan harkar tsaro Kanar Yakubu Soja ne ya fitar da wannan sanarwa.

Ya yi gargadi ga matasa a Zariya da su guji bude salansar baburansu a titunan garin. Duk wanda aka kama zai dandana kudarsa.

Share.

game da Author