A wata sanarwa da hadaddiyar kungiyoyin matasan Arewa ACYF suka fitar sun ba duk wani dan kabilar Igbo da ke zama a yankin watanni uku da ya tattara inashi-inashi ya fice daga duk wani kusurwar na yankin Arewa.
Bayan haka kuma kungiyoyin sun ce mutanen arewa zasu karbi mallakin duk kaddarorin yan kabilar idan suka tashi.
Kungiyoyin sun ce sun gama shiri kaf kuma babu wanda zai hana su aiwatar da wannan shiri na su.
Shugaban Kungiyar ACYF, Yerima shettima ya ce ayyukan kungiyar Biafra musamman na kwana-kwanan nan inda suka umurci duk wani dan kabilar Ibo ya zauna a gida barazana ce ga kasa Najeriya.
“ Muna kira ga duk wani dan Arewa da yake yankin Kudu maso Gabas da ya fara shirin dawowa gida. Kowa ya dawo cikin wadannan watanni da muka ba da.
“ Abin da zamu fara yi bayan watanni uku da muka diba wa ‘yan kabilar Igbo ya cika shine mu mallaki duk wani abin da suka kafa a yankin Arewa.
Sannan kuma kungiyoyin sunce kada gwamnatin tarayya ta dauka wannan kira da su keyi wa ‘yan kabilar Ibo wasa ne.
Shugaban kungiyar Kabilar Igbo Ohaneze Ndigbo yayi kira ga jami’an tsaro da su tasa keyar Yerima saboda irin wannan kalamai da yayi kan ‘yan kabilarsa.
Ya yi kira ga jami’an tsaro da su tabbata sun bi diddigin wannan kalamai na barazana da ya fito daga kungiyar AYCF domin ba abin ayi masa burus bane.
Wadanda suka sa hannu a wannan sako sun hada da Nastura Ashir Sharif na (Arewa Citizens Action for Change); Alhaji Shettima Yerima na (Arewa Youth Consultative Forum); Aminu Adam na (Arewa Youth Development Foundation); Alfred Solomon na (Arewa Students Forum); Abdul-Azeez Suleiman na (Northern Emancipation Network), da kuma Joshua Viashman, wanda shine ya sa hannu a madadin kungiyar Northern Youth Vanguard.