Rundunar ‘Yan sanda za suyi atisayi a Abuja

0

Rundunar ‘yan sanda a Abuja, ta bayyana cewa a ranar Asabar 17 Ga Yuni, 2017, za su yi atisayi a Abuja. Sai dai sanarwar da suka fitar ta ce kada kowa ya firgita, domin atisayi ne za su yi saboda kara gwada karfi da dabarun kwantar da tarzoma.

Daga nan sai suka shawarci musamman mazauna yankunan Nyanya, Karshi da kuma Jikwoyi da su kwantar da hankali domin su ne rugugin wutar zai fi buwaya, kasancewa su ne suka fi kusanci da filin da ‘yan sandan ke yin atisaye.

Sanarwar da kakakin yada labaran ‘yan sanda na kasa ya bayar, ya ce za a gudanar da atisayen ne tun daga 7 na safe har zuwa 4 na yamma.

Mista Omorodion ya kuma ya kunnen mazauna wadancan yankuna da ya ambata a sama da su kaurace wa kusantar wurin da za a gudanar da atisayen a tsawon lokutan da ya bayyana.

Share.

game da Author