Mataimakin kwamishinan ‘yan sandar jihar Kogi Abba Kyari ya sanar da cewa jami’an sa sun kama wasu barayin mutane da suka addabi mutanen jihar.
Ya ce sun sami tabbacin cewa kungiyar masu yin garkuwa da mutane a jihar mazauna garin Ankpa ne wanda aka samu da hannu wajen sace wani limami mai suna Jibirin Idris a kauyen Enabo dake karamar hukumar Ankpa jihar Kogi a ranar 2 gawatan Faburilu.
Ya kuma ce ‘yan kungiyan sun sako Jibirin Idris bayan sun karbi makudan kudi daga wajen ‘yan uwan limamin.
‘’Bayan tsawon watanni uku ana gudanar da bincike domin gano inda masu yin garkuwa da mutanen suke an gano cewa bayan sun karbi kudin sun gudu zuwa garin Enugu
‘’Mun kama su a ranar 29 gawatan Mayu a garin Mile 9 dake jihar Enugu’’.