Wani mazaunin Unguwan Kawo dake garin Kaduna ya ce rashin wutan lantarki da ake fama dashi a garin Kaduna musamman a Unguwannin Kawo, Unguwan Dosa, Badarawa da Unguwan Mando ya sa wannan Sallar tayi masa Kyau.
Rabiu Bala dai yana da shagon siyar da Kayan waya ne sannan kuma yana da ‘yar janaretarsa da yake caja wa mutane wayoyinsu.
Da nake zantawa da Rabiu a shagonsa, na ganshi cikin nishadi da annashuwa, yana ta fara’a kamar sabon ango, da na tambayeshi sai ya ce mini wannan janareta nda ya ke da ita ta kawo masa kudin da ya bukata a wannan Sallah gashi har yanzu ma yana ci gaba da amsar kudaden masu neman yin cajin batiran wayoyinsu.
“ Ina karbar daga naira 30 zuwa har 100, domin wani yakan baka har fiye ma. Yanzu dai kaga akwai wayoyi sama da 50 a shagonnan da nake cajinsu kuma ina zaune anan ake kawo su. Iya ka in kunna janareto na in makalasu su ci gaba da caji.
“ Matsalar rashin wutan nan ya fara ne tun makonni biyu da suka wuce a wadannan unguwannai namu kuma kaga rayuwa sai da waya yanzu, waya kuma sai da caji , caji kuma sai da wuta, idan babu na NEPA kaga dole sai da irin wannan Janareta.
“ A gaskiya Alhamdu lillahi domin na samu ciniki sosai kuma sallah ta sai dai ince Allah maimaita mana.