Rashin Lafiyar Buhari: Babu wani rudanin shugabanci -Fadar Shugaban Kasa

0

Babban Mai Taimaka Wa Shugaban Kasa kan yada labarai Garba Shehu, ya yi watsi da wani rubutu da wani marubuci ya yi, wanda ya nuna cewa an yi wata cukurkudaddar yarjejeniya dangane da shugabancin kasar nan, wadda za ta iya raba kan kasar.

Malam Garba Shehu, ya yi watsi da rubutun wanda Max Siollun ya yi a matsayin ji-ta-ji-ta kawai, wadda aka buga a wata mujalla mai suna Foreign Policy, da ke Amirka.

Shehu ya jaddada cewa marubucin ya kirkiri karya ne kawai shaci-fadi dangane da rashin lafiyar shugaban kasa da kuma halin da kasar ke ciki a hannun mataimakin sa Yemi Osinbajo wanda ya bar wa mulki kafin ya tafi.

“In banda son ya rudar da mutane, don me zai kwatanta rashin lafiyar marigayi ‘Yar’Adua ta ta Shugaba Buhari?” Shehu ya ce yanayin ma kwata-kwata ba Iri daya ba ne.

Ya kara da cewa shi fa Shugaba Buhari kafin ya koma Ingila ya bayar da mulki a matsayin riko ga mataimakinsa kamar yadda doka ta tanadar.

Ya yi nuni da cewa shi kuwa ‘Yar’Adua ai lokacin da rashin lafiya ta ci karfin sa, ai ba shi ma da sukunin iya mika mulki.

Don haka ya ce tunda Buhari ya mika mulki a hannun mataimakin sa, to maganar cewa ya bar gibin shugabanci wanda hakan zai iya harfar da rudanin shugabanci, bai ma taso ba.

Don haka sai ya ce jama’a su daina kitsa rudani da karairayi, tunda mataimakin Shugaban Kasa ya na gudanar da aikin sa babu wani cikas.

Share.

game da Author