RANAR QUDS: ‘Yan shiite da mazauna Unguwar Tudun wada sun yi arangama a Kaduna

0

Kamar yadda suka yi sanarwa ranar Alhamis din da ya gabata cewa zasu fito domin gudanar da tattaki a manyan garuruwan kasar nan, mabiya akidar shiite da mazauna unguwar Tudun Wada musamman ta yankin Kasuwar Barci sun yi arangama da juna inda bayanai ya nuna cewa wasu sun sami raunuka da kuma hasarar dukiyoyi da dama.

Shi dai wannan tattaki ana yinsa ne duk ranar Quds in da mabiyan suke tattaki domin nuna rashin jin dadinsu ga kasar Israila da ta mamaye kasar Palestine.

A Kaduna bai yi wa kungiyar dadi ba duk da cewa an gudanar da hakan a wasu jihohin kasarnan ba tare da tashin hankali ba.

Kakain rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ya ce bayan sun sami rahoton rikicin rundunar ta tura jami’anta zuwa wurin da abin ya ke faruwa domin kashe wutar fitinan.

Ko da yake da shugabannin kungiyar ke ganawa da manema labarai sun ce rundunar ‘yan sanda ne suka tura matasan su kai musu farmaki a lokacin tattakin.

Duk da cewa gwamnatin jihar Kaduna da na wasu jihohi sun hana irin wannan tattaki, kungiyar ‘yan uwa musulmi, wato Shiite bas u bin wannan doka tun bayan gwamnati ta kama shugabanta Ibrahim El-Zakzaky.

Share.

game da Author