Kungiyar jama’atu Nasrul Islam Karkashin jagorancin sarkin Musulmi Dr. Abubakar Saad ta roki al’ummar musulmi da su zurfafa yin addu’oi a cikin kwanaki 10 na watan Ramadan.
Sakataren kungiyar Dr. Khalid Abubakar ne ya sanar da haka inda kungiyar tayi kira ga musulmai da su kara dagewa wajen yin addu’o’I da ciyar da marasa hali a sauran kwanakin da suka rage na watan Ramadan.
Sannan yayi kira ga musulmai da su yawaita karatun Alkurani, da yin Ibada domin dacewa da rahamar Allah.