Tun Sadiya Jubrin na karamar yarinya, babban muradin ta shi ne ta zama malamar makaranta, mai koyarwa a cikin aji. Dalili kenan ma ta shiga Babbar Kwalejin Horon Malamai ta Bauchi, inda ta samu shaidar kammala kwas na NCE.
Watanni kadan bayan kammala NCE, sai ta samu aikin koyarwa a wata makarantar firamare mai zaman kan ta.
Duk da cewa sha’awa ce ta sa ta ke son koyarwa, albashin naira dubu takwas, a wata ba zai wadaci matashiyar mace kamar ta wadda za ta daina dogaro da sai iyayen ta sun dauki dawainiyar rayuwar ta ba.
Daga nan ne kuma sai ta fara fafutikar neman wani aikin wanda ya fi koyarwar da ta ke yi albashi mai yawa, musammam ma bayan ta yi aure. Haka ta shaida wa PREMIUM TIMES.
Irin kalubalen da Sadiya ta fuskanta, kusan shi dimbin matasan da ba su da aiki ke ciki, duk kuwa da irin so da kishin yi wa Najeriya aikin da ake fama da rashin kwararru a fannonin.
Kaico! Labarin da wata kawa ta Farida, wacce mu ka gama makaranta tare ta bayar, ya fi labarin Sadiya jimami.
Farida Hassan mai shekaru 22 a duniya, ba ta samu wani aiki ba, tun bayan kammala NCE. Ta ci gaba da zama tare da iyayen ta, har lokacin da ta yi aure.
“Na nemi aiki na gaji, kai ni fa ko da mai karamin albashi ne irin na Sadiya, amma abin ya faskara. Rayuwa ta yi min kunci, har ta kai na na iya amfana wa kai na komai.” Inji ta.
Ana cikin haka sai gwamnatin tarayya ta fito da shirin SIP, cikin 2016. Nan da nan Farida da Sadiya suka bi sahun sauran matasan Bauchi, su ka yi rijistar neman aiki a karkashin shirin N-Power, kuma suka yi sa’a aka dauke su a rukunin farko.
Ko ma dai ya abin ya ke, albashin naira dubu N30,000 ai ya isa mutum ya dan biya bukatun rayuwar sa na dole.
“A gaskiya na yi matukar farin cikin samun wannan aiki, domin a yanzu ana biya na sosai, har ina dan adana wasu kudin daga cikin albashi na, yadda zan iya daukar nauyin kai na na kara karatun ba da jimawa ba.” Inji Sadiya Jubrin.
Yadda Shirin N-POWER ya Ke
Shiri ne na kai dauki ha al’umma domin saukake musu radadin saukin rayuwa, wato Social Intervention Program, SIP. wanda jam’iyyar APC ta yi alkawarin aiwatarwa a lokacin yakin neman zabe.
N-PoWER ya kasu gida hudu:
1. Shirin ciyar da makarantun firamare na gwamnati.
2. Shirin bai wa fakirai da matalauta tallafin N5,000.
3. N-POWER domin tallafa wa wadanda suka kammala karatu babu aiki.
4. Shirin inganta kananan masana’antu, inda za a tallafa wa mata, ‘yan tireda, masu sana’o’in hannu da sauran su.
Cikin 2016 gwamnatin tarayya ta ware naira biliyan 500 domin kashe su a fannin SIP. To sai dai kuma har zuwa ranar 16 Ga Mayu, har yau naira bilyan 41 kacal aka kashe a kan wannan tsari, wanda tuni N-POWER ne ma aka fi tura wa naira bilyan 26.
Daga cikin sama da matasa miliyan daya da suka cika fom, an tantance suna 701,000, inda su ma daga cikin su aka kwashi 200000 a rukunin farko. Su ne za su karbi wani tallafi na tsawon shekaru biyu, inda za su koyar, su rungumi harkar noma na zamani da kuma kiwon lafiya.
Sai dai kuma kamar yadda kakakin yada labarai na Mukaddashin Shugaban Kasa ya fadi a cikin watan Mayu, ya ce daga cikin matasan nan 200, 000, an tantance 162,024 wadanda za a rika albashin naira 30,000 duk wata a matsayin ladar ayyukan su.
An fara aiwatar da wannan shiri a jihohi tara, ciki har da Barno, Ekiti, Ogun Oyo, Kogi, Niger, Cross River, Bauchi da Kwara, kafin daga baya shirin ya watsu a sauran jihohi.
Binciken da PREMIUM TIMES ta yi, wanda za ku karanta a kasa, ya nuna irin yadda tsarin na N-POWER ke gudana a wasu jihohi uku, da su ka hada da Bauchi, Kwara da kuma Barno.
BAUCHI
Duk da cewa Sadiya da Farida sun fara cin albarkacin N-Power a jihar Bauchi, har su na murna, da dama a jihar su kuma ba haka abin ya ke ba.
Binciken da Premium Times ta yi ya nuna cewa har yau wasu da dama ba su ma fara karbar albashin su ba, duk kuwa da cewa an tantance su kuma an tura su wuraren aiki.
Daga cikin irin wadannan akwai Abdulrazaq Muhammad, wanda ya ce tun cikin Janairu ya fara aiki, amma har yau ko kwandala ba a taba biyan sa ba. Kuma a haka ya ke koyarwa a karantar koyon aikin kimiyya ta firamare a Bauchi.
Sai dai kuma shugaban SIP na jihar Bauchi, Manu Mansur ya shaida wa Premium Times cewa miskilolin da aka fuskanta duk daga wajen masu cike FAM ne, ba daga hukumar sa ba.
Ya ce da yawan wadanda suka shiga zauren intanet na SIP, wato portal, ba su iya cike bayanan da ake so kowa ya tabbatar ya cike su daidai ba.
“Idan dai mutum bai samu kudin sa tun daga Disamba zuwa yau ba, to kenan matsalar daga wajen sa ne.” Inji shi.
KWARA
Kusan ma a iya cewa mishkilar da ake fama da ita a jihar Kwara ta fi ta Bauchi, nesa ba kusa ba. Jami’ai sun tabbatar wa Premium Times cewa tun cikin Disamba, 2016 aka tura ma’aikata har 5,104 da aka dauka.
Sai dai kuma da yawa daga cikin su, sun shaida wa Premium Times tun daga lokacin da aka dauke su zuwa Mayu, ba su karbi ko kwandala ba.
Michael Aribisala dan shekara 28 da ya kammala NCE, kuma ba shi da aiki tun da ya gama NCE cikin 2009, ya ce murnar da ya fara da farko wai shi ya zama ma’aikacin gwamnati, yanzu ta koma kuka, tunda watanni biyar kenan na wanda ya ba shi ko kwandala a matsayin albashi.
Haka shi ma Salaudeen Abdulfatai, mai shekaru 33, ya ce tun Disamba aka tura shi wurin aiki, amma tamkar turin-je-ka-ka-mutu aka yi masa, tunda har yau ba ko sisi.
BORNO
Su kuma a jihar Barno mishkilar ta su daban ce. Da yawan su tun cikin Disamba su LA fara karbar ta su N30,000 ta ladar aiki duk wata, sai dai kuma ba su fara ma zuwa aikin ba, a bilis su ke cin kudin.
Amma fa akwai irin su Muhammed Shettima, wadanda har yau ba su fara karbar na su kudin ba. Amma fa an tura shi firamare ya na koyarwa tun a cikin Mayu.
Shugaban zauren intanet, wato portal na SIP a Barno, Babazanna Abdulkarim, ya tabbatar wa Premium Times cewa sama da ma’aikata 4000 na samun na su albashin.
Kamar a sauran jihohin, shi ma Abdulkarim ya dora laifin wadanda ba su ganin ‘alert’ na shigar kudin su a duk wata, cewa laifin su ne da ba su cika fam a daidai kan ka’ida ba ta intanet.
“Sau da yawa wasu ko an tura musu kudin ta banki, ba su shiga sai su koma, saboda bayanan da suka cika na asusun ajiyar su a banki, sun sha bamnan da bayanan da suka cika lokacin cika fam na N-Power a intanet.
Kodinatan shirin N-Power na kasa, Afolabi Imoukhuede, ya ce akwai dalilai da yawa da ke sa wasu da aka dauka aikin ba su samun albashin su.
Ya ce akwai matsala daga wasu jami’an, akwai rashin tuntubar wasu jami’ai da wadanda aka dauka ba su yi. Sannan kuma akwai rashin gabatar da kai da wasu ba su yi a gan su ido-da-ido. Sai kuma matsalar da wasu ke bayar da lambar BVN ta asusun ajiyar mutum ta banki wadda ba daidai ba.
Sai dai kuma duk da irin wannan kalubale da ake fuskanta, Sadiya matar Jubrin ta bayyana wa Premium Times cewa, ” Ban ma san iyakar irin godiyar da za mu yi wa gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ba.”