Ba mu yi mamakin hayagaga, hauragiya da kuma tayar da jijiyar wuya da ake yi a sassan kasar nan kan batun yinkurin ballewa da wasu ke yayatawa ba; dalili shi ne wadannan alamomi sun dade ba tun yau aka fara ba. An dade ana hankoron neman a raba kasa, korafe-korafe da zarge-zargen wani sashe ya danne wani, ga kuma munanan kalamai masu haddasa fitintinu da ake yayatawa, a wasu lokutan ma har da wanda ba ka taba tsammanin zai iya cewa uffan ba.
Kalamai dai ga su nan wadanda ka iya kawo barazana wajen kasancewar kasar nan dunkulliya daya.
Hanyoyin da kungiyar fafutikar neman kafa Biafra, IPOB ta dauka a baya-bayan nan, gami da barazanar da wa’adin da wasu kungiyoyi daga Arewa, Kudu-maso-Yamma da kuma Neja-Delta su ka bayar, dukkan su barazana ce ga dorewar zaman lafiyar kasar nan.
Abin da aka fara a matsayin waiwayen tarihin baya, sai kuma ya juya zuwa surfa wa juna zagi, tozarta juna da kuma gaya wa juna munanan kalamai. Daga nan kuma sai abin ya zarce ana neman fara yin fito-na-fito, kamar dai irin yadda sabani ya shiga cikin 1967, wanda ya yi sanadiyyar shelar kafa kasar Biafra, wanda wannan shelar ce ta haifar da yakin basasa na tsawon watanni talatin. To kada fa mu kuskura mu bari ko mu sake tayar da wata fitinar da za ta sake dawo da balbalin-bala’in da ya rigaya ya wuce, sai dai a kundin tarihi kawai.
A cikin ‘yan shekarun nan, an rika amfani da yunkurin Biafra tun daga hanya ta lalama da kuma nuna damuwa, zuwa munanan hanyoyi na rashin mutunci da kuma dalilai na munanan bukatun siyasa.
Wannan mataki kuwa bai tsaya kan ‘yan hankoron kafa Biafra ko Igbo zalla ba. A tarihin Najeriya, kowane sashe ya na kukan cewa an maida shi saniyar-ware-ga-dangi, kuma batun sai kara kamari ya ke yi a cikin lamurran siyasar kasar nan. Amma har yau Nijeriya ba ta taba yin tunanin a zauna a tattauna wannan lamari ba. Ga shi nan yanzu har abin ya kai makurar da ya kai a halin yanzu.
Maimakon shugabannin siyasa da sauran shugabannin al’umma su taimaka a kashe wutar irin wannan hauragiya, sai su ma suka rike abin a matsayin wasu hanyoyi ko hanyar cimma wasu bukatu na su na siyasa a wurin al’ummar su, wanda hakan alamomi ne masu nuna irin yadda manyan mu ke shiga cikin shirgi su na taya bera bari.
Abin ya kara muni ganin yadda gwamnatocin da suka gabata su ka ki maida hankali wajen duba wadannan korafe-korafe a cikin kasar nan, wannan kuwa shi ya kara haifar da wutar hasala da kuma rashin bai wa gwamnati amanna. Kiraye-kirayen da aka sha yi domin a sake zama a yi nazarin tafarkin siyasar kasar nan a matsayin hanya daya da za ta maganace ka-ce-na-ce, bai samu karbuwa ba har a wurin gwamnati mai ci yanzu, wadda a cikin shirye-shirye da alkawurran da ta yi a wajen kamfen, har da batun sake duba alkiblar siyasar mulkin Najeriya.
.
Mu a Premium Times, mu na duban tayar da jijiyar wuyan da ake yi a yanzu a matsayin babbar matsala. Najeriya dai ta kowane duk dan Nijeriya ce. Don haka bai yiwuwa wani ya kawo wa wani dan Najeriya wata barazana a duk inda ya ke zaune. Dokar kasar nan ta bai wa kowane dan Najeriya cikakken ‘yanci, kuma bai yiwuwa wani haka kawai ya dakile wa wani wannan ‘yanci da doka ta ba shi. Haka kuma kowa na da ‘yancin yin magana, amma ba tare da ya take hakki ko ya shiga hakkin wani ta hanyar yayata kalamai na kiyayya ga wani ko wasu ba.
Mu a PREMIUM TIMES mun yi amanna da kasancewar Najeriya a matsayin kasa daya, al’umma daya. Amma kuma mun hakkake da cewa wannnan dunkulewa za ta fi karfi da karko idan muka duba mudubi mu ka ga irin tabo da kwarzanen da ya bata mana fuskokin mu. Lokaci ya yi da za a zauna a cikin lumana a duba wadanan korafe-korafe da kowa ke yi, domin a magance su.
Amma a cikinn hanzari, ya kamata gwamnati ta gaggauta yin maganin duk wani annaminin da ke ruruta wutar gaba da kiyayya da juna. Nijeriya ta samu kanta cikin irin wannan rikita-rikita a baya, bai kuma kamata mu zuba ido sai wannan hayaki ya zama wuta har ya fara ci bal-bal, sannan mu fara kururuwar neman agajin kashe gobara.
Lokaci ya yi da za a sake kakkabo rahotannin da aka tattara a Taron Makomar Kasa na 2014, domin magance duk wata matsalar da ke kawo mana barazana, ta hanyar sake fasalin tsarin mu na Fedaraliyya. Sai dai kuma mu na sane kuma mu na yin duba da cewa wannan ba abu ne da ba zai yiwu a cikin sauki ba, har sai idan shugabannin mu da sauran ‘yan Najeriya sun sa kishi na gaskiya har zuci, ba wai a zauna ana kallon juna, amma kowa ta-ciki-na-ciki ba.