Mukaddashin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo ya sanya hannu a kasafin kudin 2017 da yamman Litinin din yau.
Za a kashe sama da naira triliyan 7 a kasafin kudin.
Shugaba Muhammadu Buhari ya bai wa Osinbajo damar rattaba hannu kan kasafin kudin ne bayan ya gamsu da bayanan da aka bashi akan kasafin da majalisa ta amince da shi.
Mataimaki na musamman ga shugaban kan watsa labarai, Malam Garba Shehu, ya ce shugaba Buhari ya ba Osinbajo umarnin hakan ne, bayan da aka ba shi cikakkun bayanai kan abin da kasafin kudin ya kunsa.