NEMAN SULHU: Ganduje ya roki majalisar wakilai ta yafe wa Abdulmumini Jibrin

0

Gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje ya saka baki don ganin majalisar wakilai ta yafe wa dan majalisa Abdulmumini Jibrin da ta dakatar tun a shekarar bara.

Abdulmumii Jibrin dai ya shiga tsaka mai wuya ne tun bayan rashin jituwa da ya shiga tsakaninsa da Kakakin Majalisar Yakubu Dogara.

Abdulmumini ya zargi shugaban majalisar da makarrabansa da yin coge a kasafin kudin 2016.

Hakan baiyi wa shugabannin majalisar dadi ba inda bayan gudanar da bincike akan haka majalisar ta amince da ta dakatar dashi har na tsawon kwanaki 181.

Ko da yake shi Abdulmumini ya kafe akan cewa kakakin majalisar ba mutum bane mai gaskiya kuma ya na ta fitar da bayanai da zasu nuna gaskiyarsa hakan dai bai haifar masa da da mai ido ba domin yadda kasan yana magana ne da dutse.

Daga baya yayi ikirarin wai wasu na neman halakashi inda yayi kaura zuwa kasar Britaniya amma bayan dan kwanaki kuma sai gashi ya dawo mahaifarsa.

Gidan Jaridan PREMIUM TIMES ta jiyo cewa gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje dai ya sa baki akan hakan yanzu inda ya gaiyace shugaba mai tsawatarwa na majalisar wakilai Ado Doguwa da ya halarci wata ganawa ta musamman domin sama wa Abdulmumini mafita sannan ya roki majalisar da ta yafe masa laifukansa ta amince ya ci gaba da halartar zaman majalisar.

Bayanai sun nuna cewa gwamnan jihar Kano din ya gana da Kakakin Majalisar akan hakan.

Share.

game da Author