Neman abinci da magani ne ya sa Boko Haram suka kawo farmaki kauyen Kuda-kaya – Mazauna Garin

0

Wasu mazuna kauyen Kuda-kaya sun ce yan Boko Haram sun shigo garin nasu ne domin neman abinci da magunguna.

A ranar Asabar din da ya gabata ne Kungiyar Boko Haram ta kai hari kauyen Kuda- Kaya dake garin Madagali a jihar Adamawa

‘’Da suka shigo sai suka fara ihu da harbi a iska wanda hakan ya jefa mutane cikin rudani’’

” ‘yan farauta ne su ka yi artabu da su a lokacin da suka shigo. Sai dai kusan dukkan mazauna kauyen sun gudu a lokacin zuwa kauyen dake kusa da mu.”

Shugaban karamar hukumar Madagali Yusuf Muhammed ya jinjina wa ‘yan bangan kauyen da irin jarumtar da suka nuna wajen fatattakan ‘yan Boko Haram wanda hakan yasa abin ya zo da sauki.

Bayan haka kuma ya yabi jami’an tsaro da daukin da suka kawo cikin gaggawa a lokacin da abin ya ke faruwa.

Share.

game da Author