Najeriya za ta hada hannu da kamfanin sarrafa magani na May&Baker don kafa kamfanin da za a dinga sarrafa allurar rigakafi da kasa ke bukata daga 2017 zuwa 2021.
Ministan kiwon lafiya Isaac Adewole ne ya tabbatar da hakan wa manema labarai bayan kammala taron majalisar zantaswa ranar Laraba wanda Mukaddashin Shugaban Kasa Yemi Osinbanjo ya shugabanta.
Adewole ya ce gwamnatin tarayya za ta dauki kashi 49 bisa 100 ita kuma kamfanin May&Baker za ta dauki kashi 51 na kamfanin.
Ministan ya kuma ce kasa Najeriya ta kusa kawo karshen cutar Sankarau wanda ya bullo tun a watan Nuwanbar 2016 sannan kuma ya yi magana akan yadda kamfanin jirgin saman kenya ta shigo da gawan wani da ake zargin yana dauke da cutar Ebola.