Gidauniyar ‘Preston Development Foundation’ PDF ta shirya wani taro a Abuja a ranar Alhamis domin wayar wa mutane kai game da illolin da ke tattare da yi wa mata kaciya.
Domin nuna wa mutane rashin jin dadin su da irin munin da yi wa mata kaciya ya ke da shi jami’an Gidauniyar da suka halarci taron sun kwatanta illar da kaciya ke yi wa mata musamman lokacin haihuwa ta hanyar kwanciya a kasa rashe rashe.
A sakamakon binciken da Kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO ta fitar ya nuna cewa mata miliyan 40 ne akayi wa kaciya a Najeriya wanda hakan ya ke nuna cewa Najeriya ce tafi yawan matan da akayi wa kaciya a duniya.
Shugaban shirye-shiirye na gidauniyar PDF Zikar Elendu ta ce sun shirya wannan taron ne saboda wayar da kan ‘yan Najeriya ganin cewa har yanzu ana yi wa mata kaciya a kasar.
Ta kuma shawarci gwamnatin Najeriya da ta saka tsauraran matakai don hana yi wa mata kaciya musamman a asibitocin kasarnan.
” Kwanciyar da muka yi muna kwatanta illar da yi wa mata kaciya yake kawowa musamman lokacin haihuwa. Mafi yawan mata na rasa rayukansu saboda kaciyar da aka yi musu sannan kuma yana hana su jin dadin jima’I wanda hakan bai dace ba.”
” Gudun fadawa hanyar aikata zinace zinace na daga cikin dalilan da ya sa ake yi wa mata kaciya wanda hakan yana da nasaba da yadda rayuwa tayi wuya wa mafiyawan mutane. Garin neman yadda za a rayu sai kaga mace ta fada hali irin haka.
Wasu da ga cikin dalilan da ka iya kawo hakan sun hada da bin shawaran abokai, rashin samun isasshen tarbiyyar daga gida, shan kwaya da sauransu.