Kwamishinan Albarkatun Ruwa na jihar Kaduna, Suleiman Aliyu Lere ya yi kira ga mutanen yankin Zariya da su kwantar da hankalinsu cewa ruwan famfo zai wadata a ko ina a yankin nan da watan Oktoba.
Kwamishina Lere ya fadi haka ne da ya ke zantawa da gidan jaridar Daily Trust.
Kamar yadda jaridar ta ruwaito Lere ya fadi haka ne da yake kare gwamnati kan korafin da mazauna yankin Zariya suke yi cewa maganar ruwan Zariya har yanzu dai jiya iyau.
Mazauna garin Zariya sun ce tun da aka kaddamar da bude gidan ruwar Zariya babu wani da ya ga ruwa a famfonsa ballantana wai har ace an fice daga wahalar jiya.
Mazauna garin sunce gwamna El-Rufai dai ya yi abinda zai yi ne kawai ya kara gaba amma fa babu ruwan famfo har yanzu a Zariya.
” Mudai mazauna garin nan ne kuma mun shaida kaddamar da ruwar da akayi amma fa kamar an kaddamar da jaddada rashin ruwa ne ba samar da ita ba. Domin tun bayan hakan ba wani a unguwar mu da ya ga ruwa a famfon gidansa ko kuma a unguwar.” Inji wani Mazaunin Zariya.
Koda ya ke El-Rufai yayi ikirarin korar bakan gizon dake shan ye ruwar Zariya da alama dai shima tana neman ta gagareshi domin ruwa fa bai samu ba har yanzu.
Da yawa daga cikin mazauna garin Zariya sun ce badun Allah ya sa ana cikin damuna bane yanzu da wahalar tafi haka.
Kwamishina Lere ya fadi wa Daily Trust cewa har yanzu gwamnati ba ta kammala aiyukanta bane amma da zaran ta kammala ruwa zai wadatu a ko ina sannan kuma ya bada bayanai kan yadda gwamnati ta kasa aiyukan ruwan Zariya.
” Aikin ruwan ya kasu kashi kashi ne na farko shine kaddamar da matatar ruwar wanda akayi a watan Mayu, na biyu kuma shine binne bututun ruwa da muke yi da kuma giggina ma’ajiyar ruwa a unguwanni.
“Bayan haka kuma zamu hada gidaje da manyan bututun da aka binne sannan a sassaka na’urar daukar lissafin ruwar da aka ba da. Daga nan ne fa kowa zai fara samun ruwa a gidan sa.”
Duk da wannan bayanai da Lere yayi wasu da suka tattauna da Premium Times Hausa sunce abin da kamar wuya.
Umar Muhammad, wani dan kasuwa kuma mazaunin unguwan liman da ke Zariya ya ce su dai sun zuba Ido.
” Mu dai mu zuba ido. Amma wannan abu anya babu yaudara a ciki. Idan ansan da irin wannan shiri, Menene yasa aka gaggauta kaddamar da matatar tunda ba ruwar za a samu ba. Amma za mu basu uzuri mu ga gudun ruwar su.”