A cikin daren jiya ne yan kunar Bakin wake suka tada Bama-Bamai a jami’ar Maiduguri.
A cikin bayanan da kwamishinan ‘yan sandan jihar ya fitar mutane 16 suka rasa rayukansu a sanadiyyar harin inda wasu 13 suka sami raunuka.
Tun Karfe 10:15 na daren jiya ne akai wannan hari.