Ministan kiwon lafiya Isaac Adewole ya sanar da cewa Najeriya ta sami nasarar kauda da cutar Sankarau wanda yayi ajalin mutane 1,166 a cikin makoni 23 a jihohi 25.
Hukumar kula da yaduwar cututtuka NCDC ne ta tabbatar da haka a shafinta na twitter ranar Litini.
Kamar yadda aka sani ne cewa gwamnatin Najeriya ta sami nasaran kawar da cutar ne domin hukumar NCDC, hukumar kula da cibiyoyin kiwon lafiya ta kasa NPHCDA, ma’aikatar kiwon lafiya da kungiyoyin bada tallafi na kasashen waje sun hada karfi da karfe wajen ganin hakan ya faru.
Bincike ya nuna cewa tun da cutar ta bullo a watan Nuwambar 2016 mutane 14,518 suka kamu da cutar sannan a duk jihohi 25 wanda cutar ta bullo jihar Zamfara ce ta fi fama da cutar.
A lokacin da yake fadin nasarorin da fannin kiwon lafiya ta samu ministan kiwon lafiya ya ce’’Najeriya bata sami bullowar cutar shan inna ba a shekaran 2017, mutane bakwai sun kamu da cutar zazzabin Lasa sannan jihar Kwara ta sami saukin bullowar cutar kwalara’’.
Bayan haka shugaban hukumar NCDC Chakwal Ihekweazu ya ce sun samin tabbaci kawar da cutar sankarau ne bayan rahotannin da suka samu daga jihohi 25 da suka yi fama da cutar cewa sun sami saukin yadda mutane ke kamuwa da cutar a cikin makoni takwas da suka gabata.
Ya kuma kara da cewa hakan ya yiwu ne sanadiyyar canjin yanayin da aka shiga wato shigowar damina.
Daga karshe Chakwal Ihekweazu ya ce saboda irin nasarorin da gwamnati ta samu akan yin rigakafi wanda hukumar NPHCDA ta gudanar a jihohin Sokoto, Zamfara, Katsina da Yobe hakan ya sa gwamnati ta kara daura damara wajen tabbatar da cewa bangarorin kasar da suka fi fama da cutar sun sami alluran rigakafin cutar nan gaba kuma a kan lokaci.