Mun rage farashin fansan Abubakar daga naira 500,000 zuwa naira 200,000 – Inji Barayinsa a Sokoto

0

Mutanen da suka sace wani matashi dan kasauwa mai suna Abubakar Kakirko a gaban iyalinsa a kauyen Kikirko dake jihar Sokoto sun rage kudin fansan da suka nema daga Naira 500,000 zuwa 200,000.

Kwamishanan rundunan ‘yan sanda na jihar Sokoto Mohammed Abdulkadir ya sanar da haka wa manema labarai a jihar ranar Alhamis.

Ya ce sun sami wadannan bayanai ne bayan iyalan Abubakar sun sanar musu cewa barayin sun yi musu waya don sanar dasu ragin kudin fansa.

“Mun san cewa ‘yan garkuwan na ajiye da Abubakar a dajin Gundumi wanda ke kan babbar titin Sokoto zuwa Isah.”

Barayin na canza layin wayan tarho amma muna iya kokarin mu domin mu kama su.”

Abdulkadir ya shawarci mazauna jihar da su kai karan duk wanda ko kuma abin daba su yarda da su ba.

Share.

game da Author