Muhimman Addu’o’in biyan bukata a watan Ramadan – Imam Bello Mai-Iyali

0

TAMBAYA: Ina rokon Mallam da ya taimaka mani da wata addu’a da zan yi a sauran Kwanakinnan na Ramadan domin wata muhimmiyar Bukatata?

AMSA: Alhamdu lillah, Tsira da Amincin Allah su tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammad SAW.

Bawa yana kusantar Ubangijin sa Allah ta hayoyin ibada kamar Sallah da addu’a a cikin dare ko yini, a lokacin walwala ko kunci. Shi kuma Allah mai karban addu’ar bawansa ne, idan bawan ya rokeshi, ya maida al’amarinsa agareshi kuma ya dogara agareshi. Allah ya ce a cikin suratul-Bakara: “Idan bayina suka tambaye ka inda nike, ka ce musu ina kusa, kuma ina amsa addu’ar mai addu’a idan ya roke ni…”

Hakika Allah ya na karbar addu’a a wajen bawansa, kuma yana jinsa, yana sane da halin da yake ciki. Muhimmin al’amari anan shi ne bawa ya tsare dokokin yi da karban addu’a kuma ya dage da addu’ar domin bata faduwa kasa banza. Bawa ya yi addu’ar sa cikin kowane yare, ako wane lokaci, cikin tsananin imani da Allah da yarda da cewa Allah zai karbi wannan addu’ar tasa.

Akwai addu’o’i da yawa masu salo da- ban da-ban kuma Malamai suna bada waddanan addu’o’in duk da cewa basu da asali a sunnan Annabi SAW.

Annabi (SAW) ya ce Allah na sauka sama ta duniya a yankin dare na karshe, yana neman masu bukata ya biya musu ko masu addu’a ya karba musu. Ga kadan daga cikin kyawa-wan addu’o’i daga Annabi SAW:

1) Nana Aisha Allah ya kara yarda da ita, ta tambayi Annabi SAW, a yayin da na dace da daren Lailatul – Kadari me zan ce? Sai Annabi ya ce , ki ce: ALLAHUMMA INNAKA AFUWUN TUHIBBUL AFUWA FA’ AF’ANNI.
اللَّهُمَّ إِنَّكَ عَفُوٌّ تُحِبُّ العَفْوَ فَاعْفُ عَنِّي

2) Annabi SAW ya ce: Addu’ar Annabi Yunusa (AS) babu wani Musulmi da zai ruki Allah da ita, fa ce Allah ya biya bukatarsa. Addu’ar it ace: LA ILAHA ILLA ANTA SUBHANAKA INNI KUNTU MINAZ-ZALIMINA.
لَا إِلَهَ إِلَّا أَنْتَ سُبْحَانَكَ إِنِّي كُنْتُ مِنَ الظَّالِمِينَ

3) Annabi SAW ya ce: Addu’a da sunan Allah mafi girma karbabbiya ce: ALLAHUMA INNI AS’ALUKA BI ANNA LAKAL HAMDU, LA ILAHA ILLA ANTA WAHDAKA LA SHARIKA LAKA, ALMANNANU, YA BADI’AS SAMAWATI WAL ARDI, YA ZALJALALI
WAL IKRAMI, YA HAYYU YA KAYYUMU, INNI AS’ALUKAL JANNATA, WA A’UZU BIKA MINNANNARI.

اللهمَّ إني أسالُك بأنَّ لك الحمدُ، لا إله إلَّا أنتَ وحدَك لا شريكَ
لك، المنّانُ، يا بديعَ السماواتِ والأرضِ، يا ذا الجلالِ والإكرامِ، يا
حيُّ يا قيومُ، إني أسالكَ الجنة، وأعوذُ بك من النارِ

Allah muke roko ya biya bukatummu da naku baki daya. Amin.

Share.

game da Author