Matsaloli 10 dake tarwatsa hadin kan Najeriya

0

Sanata mai wakiltan Kaduna ta tsakiya Shehu Sani ya yi kira ga gwamnati da mutanen Najeriya da a fa yi takatsantsan da yadda abubuwa ke ta faruwa a kasar wanda ba abune da za a so a fadi sau biyu ba.

Sanata Shehu Sani ya zayyano wasu ababe guda 10 da sune sanadiyyar kawo ire iren matsalolin da kasa ke fama dasu.

1. Dogaro da kasar ta yi da wata sashe wajen samar mata da kudaden shiga sannan akayi watsi da sauran sassan kasar da abinda za a iya tatsowa daga yankunan.

2. Mantuwa da aka yi da irin yanayin da kasa ta fada a lokacin yakin basasa.

3. ‘Yan siyasa na yin amfani da bambancin addini, kabila, matsuguni domin raba kawunan mutane don cimma wani buri da suka sa a gaba.

4. Yadda kishin kasa ke ficewa a zukatan mutane wanda hatta ranar da kasa ta samu ‘yancin kai yanzu bai zama abinda muke dauka da mahimmanci ba.

5. Rashin samar da ingantacciyar shugabanci da gwamnatocin baya suka yi da kuma matsalar koma bayan tattalin arzikin kasa wanda haka ya kara fadada gibin dake tsakanin talakawa da attajirai.

6. Rashin samar wa matasa aikin yi da ayyukan banga da yayi Kamari a wannan lokaci sannan kuma da rashin maida hankali wajen neman bayanai da sanin tarihi.

7. Yadda aka maida aikin gwamnati da kudaden jama’a tumbin giwa. Kowa ya zo ya dibi yadda yake so maimakon a yi amfani dasu domin gyara kasa da yin tattali domin gaba.

8 Kyale wadansu shirye-shirye na gwamnati da ka iya sa a samu da hadin kan mutanen kasa an barsu duk sun lalace kamar Hukumar NYSC da makarantun FGC.

9. kiraye kiraye da wasu yankunar kasar ke yin na a ba su kasarsu.

10. Banbancin da ke tsakanin attajiran kasa wanda basu wuce cikin cokali ba da dandazon talakawar kasar.

Share.

game da Author