Majalisar Tarayya na da ikon yi wa kasafin kudi katsalandan -Dogara

0

Kakakin Majalisar Tarayya, Yakubu Dogara, ya bayyana cewa Majalisar Tarayya na da ikon tsoma hannu cikin sha’anin kasafin kudi ta hanyar kara wasu ayyuka ko kuma cire wasu da ta ke ganin ya kamata a cire su.

Dogara ya bayyana haka ne a yayin da ya ke maida bayani dangane da wani kudiri da dan majalisa Lawal Abubakar daga Adamawa ya gabatar. Abubakar, wanda dan APC ne, ya kawo wani ikirari da ya ce Mukaddashin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo ne ya yi furicin sau sau biyu a wurare mabambanta.

Ya ce da kunnen sa ya ji kuma ya karanta inda Osinbajo ya ce Majalisar Tarayya ba ta ikon yi wa kasafinn kudi katsalandan kafin a amince da shi.

Dogara ya ce ai dokar kasa ta fayyace wa kowane bangare na gwamnati irin ayyukan da zai rika gudanarwa. Kuma wannan dokar ta bai wa majalisa ikon sa hannnun ta a sha’anin kasafin kudi domin ragewa, karawa ko kuma yin wasu gyare-gyare da suka kamata.

Ya ce wani ma abin lura shi ne, wannan doka ta bayyana cewa rashin aiwatar da tsare-tsaren kasafin kudi kan sa babban laifin yi wa doka karan-tsaye ne, kuma akwai hukuncin da dokar ta tanadar ga wanda ko bangaren da ya aikata haka.

” Dukkan mu mutane ne masu kima da mutunci. Daga bangaren majalisar har bangaren gudanarwar, duk mu na ga kima da sanin darajar dokoki dadin dadawa kuma duk mu na sane da rantsuwar da muka yi cewa za mu gudanar da ayyukan mu. Ka ga ashe a fannin zartarwa, idan ba su aiwatar da wadannan kudirorin da suka yi rantsuwa a kan su ba, sun san abin da doka ta tanadar musu.’’ Inji Dogara.

Dagara ya kara da cewa ai doka ta bada damar cewa a duk inda bangaren zartaswa ya ki aiwatar da wani kudiri wanda majalisa ta tabbatar da shi a matsayin doka, to alhakin majalisa ne ta tankwara bangaren zartaswa domin biyan bukatar al’umma.

Share.

game da Author