Kungiyar ma’aikatan kananan hukumomi na kasa ta ce za ta fara sa kafar wando daya da duk wata gwamnati da ki biyan basukan da ma’aikatan kananan hukumomi da malaman kananan hukumomin ke bin ta.
Sakataren kungiyar na Kasa Chukwuemeka ne ya sanar da hakan ga manema labarai a Benin, jihar Edo. Ya ce kungiyar sa ba za ta zuba ido ta bari gwamnatoci su ki biyan ma’aikatan ba ganin cewa kwananan ne gwamnatin tarayya ta basu kudaden Paris Club domin biyan basussukan ma’aikatan kananan hukumomi, malamai da ‘yan fansho a jihar.
Ma’aikatan kananan hukumomin kasar nan da yawa dai suna fama da rashin albashi na tsawon watanni saboda kukan rashin kudin biyansu da gwamnoni ke yi.
A wasu jihohin ma da yawa sun kwashe watanni 4 babu albashi saboda matsalar hakan.
Sakataren yace idan da sun amince da hakan yanzu babu dalilin ci gaba da rike wa ma’aikatan albashi tunda a sakar musu kudade.