Gwamnan Jihar Kaduna Nasiru El-Rufai ya sanar ma wasu tawagar ‘yan Kabilar Igbo da suka ziyarce shi a gidan gwamnati da ke Kaduna cikin wannan makon cewa komai daren dadewa sai ya tabbatar an kama wadannan matasan da sukayi yi wa ‘yan kabilar Igbo barazanar su koma yankinsu.
A wata sanarwa da hadaddiyar kungiyoyin matasan Arewa ACYF suka fitar ranar 7 ga wata Yuni sun ba duk wani dan kabilar Igbo da ke zama a yankin watanni uku da ya tattara inashi-inashi ya fice daga duk wani kusurwar na yankin Arewa.
Bayan haka kuma kungiyoyin sun ce mutanen arewa zasu karbi mallakin duk kaddarorin yan kabilar idan suka tashi.
Kungiyoyin sun ce sun gama shiri kaf kuma babu wanda zai hana su aiwatar da wannan shiri na su.
Shugaban Kungiyar ACYF, Yerima shettima ya ce ayyukan kungiyar Biafra musamman na kwana-kwanan nan inda suka umurci duk wani dan kabilar Ibo ya zauna a gida barazana ce ga kasa Najeriya.
Awoyi kadan bayan fitar da wannan zantuka, Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya soki wannan kira inda ya ce ya umurci jami’an tsaron jihar da su taso kyar wadannan matasa sannan ya shirya lauyoyin da zasu shigar da su kotu.
Ko da yake hakan baiyi wa da yawa mata san Arewa dadi ba, farfesa Ango Abdullahi ya fito karara domin nuna goyon bayansa ga wadannan matasa in da ya ce yana bayan su 100 bisa 100.
Da yake zantawa da shugabannin yan kabilar Igbo din El-Rufai yace bayan kokari da yake yi na kamo duk wanda ya sa hannu a wannan takarda ya shaida musu cewa duk wanda ya ke zama a kaduna ya zama dan Kaduna ko daga ina ko yake.