Ko ka bi dokar hana kiwo a jihar Benue ko ka bar jihar – Gwamna Ortom

0

Gwamnan jihar Benue Samuel Ortom ya gargadi mutanen jihar musamman makiyaya cewa gwamnati na nan akan bakanta na hukunta duk wanda ya karya dokar hana kiwo a fili a jihar.

Gwamna Ortom ya ce gwamnati ta kirkiro da wannan doka ne domin samarda zaman lafiya mai dorewa a jihar musamman tsakanin Fulani makiyaya da manoma.

Bayan haka ya ce duk wanda ya ga ba zai iya bin wannan doka ba yana iya barin jihar.

Ortom ya fadi haka ne da yake bakuntar Kungiyoyin kiristocin Najeriya CAN da na musulmai reshen jihar da suka ziyarce shi a Makurdi.

Ya kuma kara da cewa jami’an tsaro a shirye suke da su hukunta duk wanda ya karya wannan doka idan ta fara aiki.

Dokar hukunta duk wanda ya karya dokar zai fara aiki ne daga watan Nowambar wannan shekara.

Shugabannin addinan biyu Akpen Leva da Sheikh Bala Ibrahim sun yaba wa gwamnatin jihar kan samar da irin wannan doka.

Sun yi kira ga mutanen jihar da makiyaya su marawa gwamnatin jihar baya don samar da dawwamammiyar zaman lafiya a jihar.

Share.

game da Author