Farfesa Bilikisu Shinkafi ta shawarci maza da idan za suyi aure su auri matan da suke da ilimi.
Bilkisu tace hakan zai inganta tarbiyyar ‘ya’yan da suka haifa sannan sannan kuma zai taimaka wajen rage miyagun aiyukkan da matasa ke aikatawa a kasar.
Ta fadi haka ne da take bada nata jawabin a taron da wata kungiya mai zaman kanta ta shirya mai suna ‘Zamfara Circle’ a jihar Zamfara.
Farfesa Bilkisu Shinkafi ta kara da cewa macen da bata da ilimi yak an zama matsala babba wajen tarbiyar ‘ya’ya su zamo nagari.
Ta ce macen da tayi makaranta za ta tarbiyartar da danta yadda ya kamata, zata bashi kula, da kuma koyar dashi hanyoyin da zai iya neman na kansa da Sauransu.
Ta kuma kara da cewa ilimantar da ‘ya mace zai taimaka wajen rage matsalolin da fannin kiwon lafiya ke fama da shi wanda ya hada da mutuwar jarirai, mutuwar uwa musamman wajen haihuwa, zuwa asibiti domin samun ingantacciyar kula wa yara da sauransu.
Babban bako a taron Abdullahi Shinkafi wanda shine sakataren gwamnatin jihar Zamfara ya ce a shekarun da suka gabata jihar ta sami matsalar koma baya a fannoni da yawa. Sannan ya shawarci mutanen jihar da su hada hannu da gwamnatin domin kawar da matsalolin da jihar ke fama da su.