Ministan Harkokin Wajen kasar Qatar Mohammed bin Abdulrahman al-Thani ya cesa ba za ta iya cika sharuddan da kasashen Larabawa suka nemi ta cika ba nan da kwanaki 10 masu zuwa.
Ministan yace wadanna sharudda 13 ba abu ne wanda idan ma har wai za a yi su a yi cikasu cikin kwanaki 10 ba.
Kasashen Saudiyya da Bahrain da Masar da kuma Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) sun bukaci kasar Qatar ta cika wasu sharudda 13 domin kafin su amince da ci gaba da hulda da ita ciki har rufe shahararriyar gidan talabijin na Al Jazeera.
Ckin bukatun akwai dakatar da hulda da kasashen Irn, da Iraqi da kuma rufe wani sansanin sojan saman kasar Turkiyya.
Kasashen sun zargi kasar Qatar da goyon bayan ta’addanci wanda kasar ta musanta.
Mohammed bin Abdulrahman al-Thani ya ce abin da kasashen suke bukata daga kasar Qatar ba zai yiwu ba.
Kasashen Turkiyya da Morocco sun yi jigalan abinci zuwa kasar Qatar din a wadannan kwanakin.
Discussion about this post