Kannywood na shirin sakin wasu manyan finafinai ranar 26 ga watan Yuni

0

Bayan hutu da aka sha na rashin finafinai, masu shirya finafinan Kannywood sun kammala shiri tsaf domin sakin wasu daga cikin manyan finafinai da ake ta yi musu jiran tsammani.

A cikin fina-finan da za ta saki sun hada da fim din da shaharariyar ‘yar fina-finan Hausa nan wanda yanzu ba ta tare da kannywood Rahama Sadau ta yi mai suna ‘RARIYA’.

Idan ba a manta ba kwanakin baya Rahama Sadau ta bude filin gasar rawar wakar fim din Rariya a shafinta na instagram inda duk wanda ya burge a rawan zai/zata sami kyauta.

Ana sa ran Rahama za ta sanar da wanda ya lashe gasar a ranar da za a fara nuna fim din Rariya a gidajen Kallo.

Fim din ‘MANSOOR’ na Ali Nuhu shima zai fito a ranar.

Akwai fim din ‘KANWAR DUBARUDU’ wanda Ali Nuhu ya fito da Rahama Sadau shima ana sa ran duk za su fito a wannan lokaci.

Shahararren fim din nan mai suna ‘ABU HASSAN’ shima yana kan gaba.

Hassana Dalhat ta shaida wa PREMIUM TIMES a Kaduna cewa a gaskiya an dade ba a saki finafinai masu zafi a lokaci daya ba irin wannan karon.

“ Ganin yadda masu kallo suka sha hutu yin haka da masu shirya finafinai zasu yi yayi daidai kodan su dan more hutun Sallah idan Allah ya kaimu.”

Share.

game da Author