Mataimakin shugaban majalisar dattawa Sanata Ike Ekweremadu yace idan har ana son a sami nasarar gudanar da mulkin kasar nan yadda ya kamata ya zama dole a rage wasu bangarorin gwamnati.
Ekweremadu ya fadi haka ne da ya zantawa da manema labarai. Ya ce idan ha rana son a sami nasarar gudanar da ayyukan gwamnati kamar yadda ya kamata dole ne a rage wasu bangarori saboda girma da da yawa da suke da shi.
Da yake tsokaci akan harkar tsaro a kasar nan, y ace zai yi kyau a kyale kowace jiha ta kafa nata ‘yan sandan saboda a ganinsa matsalar tsaro a kowace jiha ta sha bambam da na wata. Yin hakan zai sa a iya shawo kan matsalar rashin tsaro da ake ta fama dashi.
Da yake wanke kansa akan kaka gida da ake ganin gwamnoni za su iya yi da ‘yan sandan, Ekeremadu ya ce idan da za ayi hakan toh za a kuma kafa wata hukuma da zai dinga kula da ‘yan sandan a jihohi.
Daga karshe ya ce dole ne a dauki wasu matakai domin samar wa mutanen Najeriya irin tsaron da suke bukata.