Gwamnonin yankin Kudu Maso Gabas sun yi kira ga ‘yan kabilar Igbo dake zama a yankin Arewa da su yi watsi da barazanar da wasu kungiyoyin matasan Arewa su kayi cewa wai su tattara su bar yankin nan da watanni uku masu zuwa.
Shugaban kungiyar gwamnonin yankin kuma gwamnan jihar Abia, David Umahi ne ya sanar da haka bayan kamala taron kungiyar gwamnonin yankin.
Bayan haka kuma ya yi kira ga gwamnonin Arewa da su tabbata sun ba ‘yan kabilar Igbo din duk kariyar da suke bukata a yankin Arewa.
Ya ce dole a dauki mataki akan irin wadannan matasan gudun kada a maimaita abinda ya faru a da.