Kada barazanar matasan Arewa ya tsorataku, ku zauna daram dam a Sokoto abinku- Tambuwal ga ‘yan kabilar Igbo

0

Gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya yi kira ga duk wani dan Kabilar Igbo dake zaune a jihar Sokoto da ya shirya ci gaba da zaman Sokoto domin kamar yadda ya ce Sokoto  ma gida ne a wajen su.

Tambuwal ya fadi haka ne a wajen wani taron bude baki da ya yi da ‘yan Kabilar Igbo mazauna garin Sokoto.

Tambuwal ya kara da cewa yana tare da shugaban kungiyar gwamnonin Arewa kan raddin da suka maida wa matasan Arewa da suka bukaci ‘yan kabilar Igbo su koma yankinsu tunda sunce su Biafra suke so.

” Kada wani dan Kabilar Igbo ya ta da hankalisa musamman idan mazaunin Sokoto ne domin babu wani da ya Isa ya taba lafiyarsa.”

Shugaban tawagar Inyamirai din ya shaida wa gwamnan cewa basu taba samun wata fargaba ba a tsawon zamansu a jihar Sokoto. Sun kuma gode wa Tambuwal da bude baki da ya gaiyacesu.

Share.

game da Author