Jami’an hukumar tsaro na sirri da na ICPC sun kai samame gidan Namadi Sambo a Kaduna

0

Jami’an hukumar tsaro na sirri SSS da na ICPC sun kai samame gidan tsohon mataimakin shugaban kasa Namadi Sambo dake Kaduna.

Jami’an dai sun isa gidan ne da karfe 3 na Yamma inda suka mika wa maigadin gidan takardan neman gudanar da bincike a gidan.

Bayan sun gama binciken da za su yi da misalin karfe 5 na Yamma ne suka tafi.

Mai magana da yawun Namadi Sambo, Umar Sani ya ce wannan shine karo na 5 da ake gudanar da irin wannan bincike a gidan maigidansa.

Ya ce Gwamnatin APC na yin haka ne don muzguna wa ‘yan adawa saboda tsoron yi musu illa a zabe mai zuwa.

Share.

game da Author