Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya aiko da gaisuwar sallah ga ‘yan Najeriya musulmai da Kristoci.
Garba Shehu ne ya sanar da haka a wata sako ta musamman daga shugaban Kasa Muhammadu Buhari.
Bayan haka kuma ya yi kira ga ‘yan Najeriya da a yi hakuri da juna a guji furta kalaman da zai iya ta da zaune tsaye ko ya wargaza zaman da ake yi na kasa daya.
Ya yi kira ga Musulmai da su yi amfani da darussan da aka koya a watan Ramadan sannan a zauna lafiya a kasa.