Hukumar kula da rage yaduwar cutar kanjamau ta kasa NACA za ta hada hannu da wasu kungiyoyi masu zaman kansu domin samar da kudaden da hukumar ke bukata don rage yaduwar cutar kanjamau a Najeriya .
Shugaban hukumar NACA Sani Aliyu ya ce Najeriya na matukar bukatan hada irin wannan kawance da kungiyar Nigeria Business Coalition Against AIDS (NIBUCCA) da kamfanin sadarwa na MTN.
Sani Aliyu ya ce hakan zai rage yawan dogaro da kasar ke yi da kasashen duniya wajen samun tallafi.
Sani Aliyu ya kara da cewa rage yadda jarirai ke kamuwa da cutar daga uwayensu tun suna ciki na daya daga cikin hanyoyin da zai taimaka wajen kawar da cutar kwata-kwata kafin shekarar 2030.
Ya bayyana cewa kowani mutum dake dauke da cutar kanjamau na bukatan kudin da ya kai Naira 50,000 domin samun kula sannan a Najeriya mata masu juna biyu 177,000 na matukar bukatan kula.
Shugakan kungiyar NIBUCAA kuma shugaban bankin Access Bank Herbert Onyewumbi ya jinjina wa hukumar NACA kan irin kokarin da ta keyi na ganin an kawai karshen yaduwar cutar Kanjamau a kasar.